Majalisar wakilan Tarayyar Nijeriya ta bukaci hukumar kwastan ta kasar da ta biya diyyar mutanen da jami’anta suka kashe da wada...
Majalisar wakilan Tarayyar Nijeriya ta bukaci hukumar kwastan ta kasar da ta biya diyyar mutanen da jami’anta suka kashe da wadanda suka raunata a fadin kasar jumullar naira miliyan 390.
Wannan na cikin shawarar da ke kunshe a rahoton kwamitin majalisar mai kula da harkokin hukumar kwastan bayan binciken da ‘yan kwamitin suka gudanar kan abin da ya faru a jihar Katsina da kuma jihar Oyo.
Kwamitin ya bayar da shawarar biyan kowane daya daga mutane 10 da ake zargin kwastan sun kashe a Jibia, jihar Katsina ranar 9 ga watan Agusta 2021, diyyar naira miliyan 20 kowanne daga cikinsu.
Su kuwa mutane 13 da suka samu raunuka a lamarina biya su naira miliyan bibbiyu domin jinya.
Kan rikicin Iseyin a jihar Oyo kuwa, majalisar ta bukaci hukumar kwastan din ta biya diyyar mutane hudu da ake zargin jami’anta sun kashe, suma naira miliyan 20 kowanne, wadanda suka ji rauni kuwa naira miliyan biyu kowa.
Haka kuma majalisar ta nemi a gurfanar da jami’an kwastan din da suke da hannu a kisan ‘yan Najeriya wadanda ba su ji ba ba su gani ba a gaban shari’a a hukunta su domin ya zama darasi ga wasu.
No comments