Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari tare da wasu ƴan sanda huɗu kan zargin ta...
Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ce ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari tare da wasu ƴan sanda huɗu kan zargin ta'ammali da hodar iblis.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar da yammacin Litinin ta ce an kama mutanen ne bisa zargin haɗa kai wajen aikata miyagun laifuka, da saɓa ƙa'idar aiki.
Sanarwar na zuwa ne sa'o'i bayan hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Nujeriya NDLEA ta ce tana neman mataimakin ƴan sandan ruwa a jallo saboda zargin ta'ammmali da hodar iblis.
Kakakin rudunar DSP Olumuyiwa Adejobi ya ce an kama mutanen ne bayan wasu bayanai da hukumar ta NDLEA ta fitar.
Olumuyiwa Adejobi ya ce tuni Babban Sufeton ƴan sandan ƙasar ya ba da umarnin gudanar da gagarumin bincike na cikin gida, kuma an gano cewa Abba Kyari na da hannu a haɗa baki da aka yi da wasu jami'an ƴan sanda da na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wajen batar da sawun hodar iblis ɗin da aka kama a filin tashin jirage na Enugu.
Tuni aka damƙa Abba Kyari da saurna ƴan sandan da ake zargi ga hukumar NDLEA don gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi.
Sanarwar ƴan sanda ta ce tuni kuma aka fara shirin ladabtar da jami'an ƴan sandan da ake zargi a cikin gida.
Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka ana tsare da Abba Kyari a sashin tattara bayanan sirri na rundunar dake Abuja.
No comments