Ƴan Wasan Kwallon Kafa Za Su Samu Karin Albashi A Zamfara


Daga Hussaini Ibrahim, Gusau

A kokarin da Gwamnatin jihar Zamfara ke yi karkashin jagorancin Gwamna Matawalle na ganin ta inganta Harkar wasannin a jihar, yanzu haka tana shirin karawa 'yan wasan karin albashi daga N40, 000 zuwa N50,000 dan kara karfafa su akan gagarumar nasara da suke samu a fagen wasannin.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin wasanni Honorabul Habib Yuguda Gusau ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.

Honorabul Yuguda ya kuma bayyana cewa, yanzu haka Gwamnati za ta kashe naira biliyan N1.5 wajen gina filin wasa na Zamani a Gusau babban birnin jihar.

 'Ya ce filin wasan idan aka kammala shi zai kasance irinsa na farko a daukacin yankin Arewa maso yammacin Nijeriya domin zai kasance mai inganci a duniya.

Ya ce gwamnatin jihar ta kuma amince da kashe Naira miliyan 100 don gyarawa da kuma sake gina filin wasa na tunawa da Sardauna da ke Gusau domin bunkasa harkokin wasanni a jihar.

Ya kara da cewa an kuma dauki sabbin ‘yan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Zamfara United domin bunkasa damarta na lashe kofi a gasar ta bana.

Honorabul Yuguda ya ce ana bai wa ‘yan wasa albashi mai kyau da alawus-alawus don bunkasa kwazon su. Habib ya ce wasanni shi ne babban fifikon gwamnatin jihar saboda muhimmancinsa ga matasa.

"Wasanni da ake yi yana kara kawo zaman lafiya a tsakanin jama'a a cikin al'umma da sada zumunci," in ji Habib.

Ya kuma yi kira ga matasa a jihar da su dukufa wajen shiga harkar wasannin na kowanne sashe da ya taimaka wajen cin moriyarsa kuma rayuwa ta inganta.

Post a Comment

0 Comments