Ƙasashen Yamma 'Daular Ƙarya Ce', inji PutinShugaba Putin na Rasha ya bayyana takunkumin ƙasashen yamma a matsayin takunkumi daga 'Daular Karya'. 

Vladimir Putin ya kira ƙasashen yamma a matsayin "daular ƙarya" ne a yayin ganawa da jami'an gwamnati da jami'an kuɗi bayan da Moscow ta fuskanci sabbin takunkumi a ƙarshen mako.

"Ni da [Firaminista Mikhail Mishustin] mun tattauna wannan batu, bisa la'akari da takunkumin waɗanda ake kira da ƙasashen Yamma - kamar yadda na kira su a cikin jawabina da 'daular ƙarya' - a yanzu dai tana ƙoƙarin aiwatar (da takunkumin) a kan ƙasarmu".

Post a Comment

0 Comments