Daga Hussaini Ibrahim Bayan awa biyar da Majalisar dokokin jihar Zamfara, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Hon. Mu'az...
Daga Hussaini Ibrahim
Bayan awa biyar da Majalisar dokokin jihar Zamfara, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Hon. Mu'azu Magarya, Babbar Jojin Jihar Zamfara, Hajiya Kulu Aliyu Anka ta rantsar da sabon Mataimakin gwamna, Sanata Hassan Nasiha Gusau.
Tun bayan kin marawa gwamna Matawalle baya da mataimakinsa Barista Mahadi Aliyu Gusau yaki yi na binsa zuwa Jam'iyyar APC ya sanya dangantakarsu ta canza, kai kace babu mataimakin gwamna a Zamfara.
Ana cikin haka kuma sai majalisar dokokin jihar ta sanya kwamitin binciken Barista Mahadi aka zarginsa da almundahana da kudaden ofishin ba bisa ka'ida ba. Wannan ya sanya 'yan majalisun mika masa babbar Jojin Jihar Zamfara sunaye kwamitin da za su bincikesu, laifukan da ake zargin mataimakin gwamna.
Bayan mako daya da babbar Jojin jihar Zamfara ta rantsar da kwamitin mutane bakwai karkashin jagorancin Halidu Tanko Soba ya mikawa Majalisar dokokin rahotansu na kammala binciken Mataimakin gwamnan ga Majalisar dokokin jihar ta Zamfara.
Sai a yau Laraba da karfe daya na rana majalisar dokokin jihar Zamfara karkashin jagorancin Kakakin Majalisar Dokokin Hon Mu'azu Magarya ta karanta rahotan kwamitin kuma ta zartar da tsige dhi nan take, kuma ta tantance Sanata Hassan Nasiha Gusau a matsayin wanda zai gaje shi.
No comments