Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Babu Kotun Da Za Ta Iya Hana Mu Tsige Mataimakin Gwamna -Majalisar Zamfara

A jiya Talata ne Majilisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta baiyana cewa babu wata dokar kotu da za ta iya hana ta tsige Mataimakin Gw...


A jiya Talata ne Majilisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta baiyana cewa babu wata dokar kotu da za ta iya hana ta tsige Mataimakin Gwamna, Mahdi Aliyu Gusau.

Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar, Shamsudeen Bosko ne ya fadi hakan a taron manema labarai a Gusau.

A ranar Litinin ne dai wata Babbar Kotun Taraiya ta gargaɗi majalisar dokokin ta Zamfara kan shirin tsige Mahdi.

Mai Shari'a Iyang Ekwo ne ya yi gargaɗin bayan da lauyan PDP, Emmanuel Ukala, SAN, da kuma shi Mataimakin Gwamnan su ka shigar da ƙara, inda su ka roki kotun da ta hana majalisar tsige shi.

Amma mai Shari'a Ekwo bai fito ƙarara ya bada umarnin hana tsige Mahdi ɗin ba.

Sai dai ya ce tunda dai dukka ɓangarori biyun sun je kotu, to ba wanda zai ɗauki wani mataki yayin da maganar ke kotu.

Sai dai kuma, a taron manema labaran,  Bosko ya ce babu wata kotu da za ta iya tsaida su da ga tsige Mahdi ɗin, inda ya ƙara da cewa, hanyar da a ka bi taa tsige Mataimakin Gwamnan ta yi dai-dai da sashi na 188(5)(7) na 1999.

A cewar sa, 18 cikin ƴan majalisa 24 sun zaɓi a tsige Mahdi ɗin lokacin da aka same shi da badakalar kudaden, rashin biyayya da kuma ƙin yin aiyukan da a ka sa shi ya yi.

No comments