Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya Usman Alkali ya bada umurnin rusa rassan runduna ta musamman da ke kai dauki wajen binciken...
Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya Usman Alkali ya bada umurnin rusa rassan runduna ta musamman da ke kai dauki wajen binciken asiri ta IRT da kuma runduna ta musamman da ke kai dauki wajen dakile aikata laifuffuka da ake kira STS.
Daukar wannan mataki ya biyo bayan kama mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da ke shugabancin bangaren IRT saboda zargin da ake masa na mu’amala da masu safarar miyagun kwayoyi.
Sanarwar da Sufeto Janar ya gabatar ta bukaci daukacin ‘yan sandan da ke aiki a karkashin wadannan bangarori guda biyu da su gabatar da kan su a cibiyar rundunar da ke Abuja.
Jaridar Premium Times ta ce Sufeto Janar ya bada umurnin sake fasalin ayyukan tsaron kasar da kuma rarraba jami’an da ke aiki a wadannan sassa biyu zuwa sauran hukumomin 'yan sanda da ke fadin kasa.
Hukumar yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta hannun kakakin ta Femi Babafemi ta zargi Kyari da taimakawa masu safarar miyagun kwayoyi da kuma gabatar da wani faifan bidiyo da aka nada wanda ke nuna yadda mukaddashin kwamishinan 'yan sandan na bayani da musayar kudade da suka shafi hodar ibilis da aka kama.
Tuni wannan labari ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Nijeriya dangane da rawar da Kyari ya taka wajen gudanar da aikinsa da kuma yadda wannan matsala ke barazana ga makomarsa a matsayin babban jami’in dan sandan Nijeriya.
No comments