BBC ta labarto cewa; wata yarinya ƴar ƙasar Faransa ta haddace Al-Ƙur'ani mai girma a cikin watanni huɗu a birnin Zaria na J...
BBC ta labarto cewa; wata yarinya ƴar ƙasar Faransa ta haddace Al-Ƙur'ani mai girma a cikin watanni huɗu a birnin Zaria na Jihar Kaduna.
Yarinyar mai suna Fatima Musa wadda iyayenta yanzu haka suna Faransa, sun tura ta Nijeriya ne domin karatu kuma ta soma haddar ne a wata makaranatar Islamiyya a Zariya inda ta rinƙa haddace shafi takwas na Al-Ƙur'ani a duk rana.
A yau ne aka yi bikin saukar haddar inda ɗaya daga cikin manyan baƙin da suka halarci saukar har da Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III da Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin Kazaure Najib Hussaini Adamu da sauran manyan sarakuna.
Hukumar makarantar ta ce wannan ne karo na farko da ta samu ɗaliba mai irin wannan hazaƙar.
Makarantar dai ta yaye sama da ɗalibai 140 da suka haddace Al-Ƙur'ani.
No comments