Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin daurin wata shida ba zabin tara a kan tsohuwar ‘yar fim din Hausa na Kannywood, kuma fitacciy...
Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin daurin wata shida ba zabin tara a kan tsohuwar ‘yar fim din Hausa na Kannywood, kuma fitacciyar mai sayar da kayn mata, Sadiya Haruna a bisa laifin batanci ga wani darekta a harkar fina-finan, Isa I. Isa.
Kotun ta majistare wadda ke zama a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, ta same ta da laifin batanci ga Darektan wanda ya kai ta kara, a shafinta na Instagram, a yau Litinin 7 ga watan Fabrairun 2022.
Kotun ta kuma zartar da cewa kada wadda aka samu da laifin ta kara wani rubutu ko sanya wani abu a wani shafinta na sada zumunta da muhawara, wanda zai zama na batanci ga wani nan da shekara daya, idan ba haka ba za a sake yanke mata wani hukuncin na shekara biyu.
Sai dai kuma Sadiya Harunar tana da damar daukaka kara kan hukuncin kotun.
No comments