Babban Bakin Nijeriya, CBN ya ce wani lokaci cikin wannan shekara zai soke saidawa bankunan kasar kudaden kasashen waje kamar y...
Babban Bakin Nijeriya, CBN ya ce wani lokaci cikin wannan shekara zai soke saidawa bankunan kasar kudaden kasashen waje kamar yadda aka saba.
Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele wanda ya sanar da haka a Abuja ya ce, za su taimakawa bankunan hanyoyin samun kudaden da kansu.
Hakan na zuwa ne bayan da asusun bada lamuni na duniya IMF ya sake yin kira ga gwamnatin Nijeriya da ta janye tallafin Man fetur da kuma cire farashin canji kudaden ketare a hukumance.
No comments