Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Cire Wasu Takunkumi Da Amurka Ta Yi A Kan Mu Bai Wadatar Ba, Inji Iran

Matakan da kasar Amurka ta dauka na cire wasu jerin takunkuman karayar tattalin ariziki da ta saka kan kasar Iran abu ne mai kya...


Matakan da kasar Amurka ta dauka na cire wasu jerin takunkuman karayar tattalin ariziki da ta saka kan kasar Iran abu ne mai kyau,  sai dai ba su wadatarwa, in ji ministan harakokin wajen Iran. Bayan da Amurka ta bayyana soke wasu jerin takunkumai da ta saka wa kasar, da ke da alaka da aikin samar da makamashin nukliyar da kasar ta Iran ke yi.

Ministan harakokin wajen kasar ta Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya sanar da taron manema labarai a Tehran cewa, ya kamata a sani,  abin da ke rubuce kan takardu ya na da kyau, sai dai bai wadatar ba, da zai sa kasar Iran ta dakatar da halastaccen aikin samar da makamshin nukiliyar da take yi wa al’ummarta ba.

Matakin da gwamnatin Joe Biden ta dauka ya kasance mai muhimmanci ga mahukumtan Tehran a daidai wannan lokaci da a birnin Vienne, a ke ci gaba da tattaunawar yinkurin ceto yarjejeniyar 2015 kan aikin Nukliyar da ke kan ganiyar karshe. 

A 2018 ne, shugaban Amruka da ya gabata Donald Trump, ya janye kasarsa daga cikin yarjejeniyar tare da maida daukacin takunkuman kariyar tattalin arizikin  da Amrukar ta kakabawa kasar ta Iran,  al’amarin da ya sa,  Iran jingine aiki da wasu fannoni na yarjejeniyar kawo yanzu da gwamnatin shugaba Biden, ta sake maido kasar kan teburin  tattaunawar neman ceto tsohuwar yarjejeniyar ta 2015 amma tare da kwaskwarima. Matakin da Iran ta ce ba ta yarda da shi ba.

No comments