Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ciwon Maraici Ne Yasa Na Bude Gidauniyar Tallafawa Marayu Da Gajiyayyu, Inji Dr. Isah Billami

Dr. Isah Billami shi ne shugaban gidauniyar Billami Education and Charity Foundation (BECF), wanda   take kokari wajen tallafawa...


Dr. Isah Billami shi ne shugaban gidauniyar Billami Education and Charity Foundation (BECF), wanda take kokari wajen tallafawa marayu da kayan karatu dama biya musu kudaden makaranta.

A cikin tattaunawa Da MANHAJA  Dr. Bulami ya kawo irin kabulabalen da suka fuskanta dama nasarori a cikin tafiyar asha karatu lafiya.

Da farko zamu so ka gabatar mana da kanka.

Assalamu alaikum sunana Isah Billami an haifeni a unguwar maidu  garin Hadejiya dake jihar Jigawa ina da shekaru 54 a duniya na kumayi makarantar firamare da sakandare  duk a garin na Hadejiya.

Na samu damar halartar Kaduna Polytechnic na samu diploma daga nan na tafi Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi nayi dirina.

Na kuma samu damar halartar kwasa kwasa-kwasai dewa a ciki da wajen kasar nan.

Yanzu haka ina aiki sannan kuma ina kasuwanci. Alhamdulillah.

Yaushe ka kirkiri wannan Gidauniyar ta BECF.

To Alhamdulillah, zance kusan bata dade ba a cikin shekarar 2021 ranar  10 ga watan goma.

Sakamakon kasancewata Maraya wanna tasa shaukin tallafa musu ya fara zuwa min a cikin Zuciyata.

Sakamakon maraici kamar yadda 'yan siyasa kance jam'iyarsu to nima jamiyatace, na taso Maraya duk da bahaushe na cewa babu Maraya sai rago.

Bayan mun yi shawara da 'yan uwa da abokanen arziki suka bani shawara suka karfafe Ni wannan tasa na fara tallafawa marayu.

Kusan na dauki ɓangare biyu ilimi da kuma jinƙai musamman marasa galihu.

Kamar yadda ka sani ilimi shine jigon rayuwa babu abinda yafi ilimi muhimmanci a rayuwar dan adam.

Haka kuma suma (less privilege)masu rangwamen karfi. Kasan mutane ne wanda suke buƙatar tallafi ko ince kulawa ta musamman saboda rashin karfi da shekaru Wannan tasa dole suna bukatar jin kai da tallafawa daga masu abin hannu.

Wadanne nasarori za a iya cewa kun samu a wannan giduniyar.

To alhamdulilah, kusan zan iya cewa zuwa yanzu mun samu nasarori a bangaren tallafawa ilimi, na farko akwai makarantar islamiyya da muka kai kayan karatu wanda kusan dalibai dari sun amfana da kayan koyo da koyarwa. haka kuma mun samu damar zuwa wata tsangaya wanda muka tallafawa almajirai da butocin alwala,bargon rufa dayake lokacin sanyi ne da kuma bokitin wanka wanda akalla almajirai kusan hamsin sun amfana da wannan tallafi.

Haka kuma ade bangaren nasara mun sami bada tallafi ga wata makarantar 'ya'yan Fulani wato Nomadic Schoolool wanda duk wanda ya sani yasan Fulani da baiwar ganen karatu wannan tasa muka tallafa musu kuma kusan yara hamsin sun amfana da kayan koyo da koyarwa.

Ta daya bangaren kuma mun  talllafawa marasa karfi ko ince marasa galihu akwai gidan masara karfi dake garin Birniwa mun samu damar tallafa musu da kayan sakawa duk da yake kusan dukkansu mata ne haka tasa muka hada musu da kayan amfani da mata suke sakawa kuma hakika sunji dadi sun mana addu'ar fatan alkairi.
Haka kuma mun samu damar ziyartar gidan gyaran hali dake garin Hadejia Correctional Centre mun kuma tallafa musu da kayan sakawa da butocin alwala da kuma Alqur'ani mai girma guda dari da kuma  

Sauran littafi da suka danganci ilimin addini dama kayan gyaran muhalli domin kulawa da tsabtar muhallansu.

Kamar yadda na fada jaririyace dole sai zuwa gaba zamuna gudanar da ayyuka manya na cigaban alummarmu.

Kusan komai na rayuwa baya tafiya saida kudi ta ina ne kuke samun kudaden gudanar da wannan aikin tallafin.

To Alhamdulillah kudi ya zama zuciyar komai na rayuwar nan babu abin da yake tafiya bate da kudi ba.hakika muna da membobi wanda wasu yan uwane na jinni wasu kuma abokanen arziki mukan tattara taro da kwabo domin yin aiki a karshe bayan mun gudanar da bincike kan tallafin sai mu cika da abinda ya samu .amma zuwa yanzu mun fara tunanin yadda zamu kirkiro hanyoyin dogarai dakai wanda zasu zama sune jigon da zasuna kula da ayyukan gidauniyar.

Babu abu a rayuwa da baya fuskantar kalubale wadannen kalubalai ne za'a hakikance kun samu.

To maganar gaskiya kalubalai kan akwaisu, na farko wasu suna mata kallo akwai siyasa a cikinta wanda kusan komai na rayuwa baya tafiya batare da siyasa ba duk da tun farko mun bayyanawa yan kungiyarmu cewa komai zamuyi muyi da iklasi wato muyi dan Allah batare da tunanin samun lada a gun wani ba haka kuma muyi hakuri da irin wadannne yarfe da za'a na jifanmu dasu.

Na biyu kamar yadda na fada muna fuskantar karanci kudi wanda kusan yana kawo mana tasgaro a wannnan tafiya duk da idan ka duba abin ba wai dewa muka far aba kadan kadan domin ya zama mun iya cinma nasara haka kuma mukan dauki duk wata uku  na shekara muyi aiki to kaga dole muna da bukatar kudi.

Wane buri kuke dashi a wannan tafiya.

To Alhamdulillah babban burinmu shi ne muna so ace mun samu damar kafa makarantar marayu da marasa karfi wanda zamu dauki nauyi karatunsu .wato basic kon ince tushe domin idan ka bada ilimin kayi sadakatu jariya ne.

Haka kuma muna da burin ci gaba da kyautatawa marasa karfi domin su zama sun samu sauki a rayuwarsu dama masu bukata ta musamman domin su zama sun samu cigaba a kashin kansu wannnan kusan baban burinmu ke nan.

Wasu suna kallo bude gidauniyar yana da bukatar makuden kudade komai nene gaskiya wannan batun.

To maganar gaskiya wannnan tunani  ba gaskiya bane, ita gidauniya ana bukatar mutum yaji cewa zai iya bawai sai ka tanaji makudaden kudade ba.

Kusan har kullum muna faɗawa mutane cewa duk wanda ya sharewa wani hawaye yaji dadi ya sani akwai dimbin lada ba kadan ba haka kuma sadakatu jariya ce wanda ko bayan ran mutum zaana rubuta masa lad aba kadan ba.to gaskiya ina kira ga masu hannu da shuni da yan kasuwarmu dasu rinka bude irin wadannnen hanyoyi domin samarwa alummarmu cigaba akwai yara masu baiwoyi dewa amma rashin karfi yakan hanasu damar yin karatu mai zurfi wanda hakan kuma ya zama cutarwa ga al'umma muyi amfani da resource din alumma mu samar da cigaba a cikin community din da muka samu kanmu a cikinsa.insha Allah zuwa gaba zamu gayyaci sauran kungiyoyi na kasa dana waje domin su shigo cikin lamarin ayi aiki tare dasu.

Wani kira kuke dashi ga matasa kan shigowa ayi irin wannnan tafiya dasu.

To a gaskiya muna kira ga matasa kusan a yanzu haka a matasa a cikin wannnan tafiya tamu babu wani abu da yake tafiya batare da matasa ba kusan sune kashin bayan alumma to kaga dole ya zama munyi tafiya hannu da hannu da matasa domin samun cigaba ga ita alumma din.
Haka kuma muna dada karfafa matasa kan muhimmanci neman ilimi domin ilimi jarine wanda idan ka rike shi zaka samu cigaba a rayuwarka a yanzu babu abinda zakayi batare da ilimi ba koda Sanaa ce idan da ilimintafi tafiya dari bisa dari.
Haka kuma muna ta kira ga matasa kan dagewa da sanaoi domin samun rufin asiri koda kayi karayu to ka hada da Sanaa zaka komai na tafiya da yardan Allah.
A karshe ina godiya da wannan dama da kuka bani Allah ya kara muku daukaka.

Mun gode. 

No comments