Cutar Korona Na Nan A Nijeriya Ta Sake Kama Mutum 36


Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta NCDC a Nijeriya ta ce ƙarin mutum 36 ne suka kamu da cutar korona ranar Lahadi.

A rahoton da ta wallafa ranar Lahadi da dare, cutar ba ta kashe kowa ba.

Jihohin da aka samu sabbin kamuwar biyar ne, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar. Su ne:

Legas - 23
Abuja - 5
Osun - 4
Taraba - 3
Nasarawa - 1

Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 253,727 ne suka harbiu da cutar a Nijeriya, sannan ta kashe 3,139 tun bayan ɓullarta a Fabarairun 2020.

Post a Comment

0 Comments