Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

DA ƊUMI-ƊUMI: Abdulmalik Tanko Ya Musanta Garkuwa Da Kuma Kashe Hanifa

Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe dalibarsa, Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, ya musanta garkuwa da...


Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da yin garkuwa da kuma kashe dalibarsa, Hanifa Abubakar, ƴar shekara 5, ya musanta garkuwa da kuma kashe ta.

A yau Litinin ne a ka sake kawo Tanko, da abokan aikata laifin da a ke zargi, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin a gaban Babbar Kotun Jihar Kano ƙarƙashin Alƙali Usman Na-Abba.

Bayan da a ka karanto musu tuhume -tuhumen da a ke yi musu, dukkan su sun musanta.

Da a ke tuhumar Tanko cewa ya yi garkuwa da kuma kashe Hanifa, sai ya ce "ban aikata ba." Kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta labarto. 

Ƙarin bayani na nan tafe...

No comments