Shugaban kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya shawarci hukumar gudanarwar kwaleji...
Shugaban
kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University, Farfesa Adamu
Abubakar Gwarzo, ya shawarci hukumar gudanarwar kwalejin ilimi ta Sa’adatu
Abubakar Rimi da ke Kumbotso da su hada kai da sauran makarantu makamantan su a
fadin duniya domin ci gaban kwalejin.
Ya
ba da wannan shawarar ne a lokacin da ya jagoranci ministan ilimi da bincike na
kimiyya na Jamhuriyar Nijar, Dokta Mamoudou Djibo wanda ya kai ziyarar ban
girma a kwalejin da ke Kano a ranar Alhamis.
Farfesa
Gwarzo, wanda kuma har wala yau shi ne shugaban kungiyar jami'o'i masu zaman
kansu a Afirka, ya lurantar da cewa haÉ—in gwiwar kasa da kasa a tsakanin
kwalejoji ko jami'o'i yana amfanar da ba kawai ma'aikata da dalibai ba har ma da
duniya baki daya.
Ya
ce akwai bukatar kwalejin ta fara tunanin yadda za ta hada kai da sauran makarantu
a fadin duniya.
A
cewarsa, daliban kwalejin za su samu abin da ya bayyana a matsayin fasahar kasashen
duniya ganin cewa za su yi mu’amala da mutane daban-daban daga bangarori
daban-daban na zamantakewa da al’adu mabambanta.
"Kwaleji
da take da ma'aikatan ilimi sama da 109 da digirin digirgir (PhD) da wasu 248 ma’aikatan
da ke da digiri na biyu (Masters) yakamata su fara tunanin haÉ—a gwiwa da
kasashen duniya. Samar da kawancen kasa da kasa da sauran kwalejoji da jami'o'i
na taimakawa ba kadan ba wajen kai makarantar zuwa ga sauran kwalejoji a fadin
duniya," in ji shi.
Ya
kuma karfafa bukatar kwalejin ta shiga tsarin musayar dalibai a tsakanin
kwalejin da sauran makarantu a jamhuriyar Nijar domin koyar da harshen
faransanci.
"Dalibai
da yawa a yanzu suna neman damar yin karatu a kasashen duniya, saboda wannan
dalili, yana da kyau jami'o'i da kwalejoji su kara yawan kulla alaka da
kasashen duniya wajen jawo hankalin masu neman karatu daga ko'ina cikin duniya.
“Shirin
musanya yana bai wa dalibai damar yin balaguro zuwa kasashen duniya a shirin
musanyar baya ga bai wa jami’o’i dama domin fahimtar al’adun sauran kasashe,”
in ji shi.
Ya
ce baya ga haka, shirye-shiryen hadin gwiwar kasa da kasa na taimakawa ta
hanyar bai wa dalibai damar yin karatu, aiki, da tafiye-tafiye a kasashen
duniya, don haka akwai bukatar kwalejin ta ba da fifiko kan harshen Faransanci.
Tun
da farko, Shugaban Kwalejin Farfesa Isa Bunkure ya shaida wa Ministan cewa
kwalejin da aka kafa shekaru 40 da suka gabata, tana da dalibai sama da 19,000,
ma’aikata 109 da ke da digirin digirgir (PhD) da kuma wasu 248 da ke da digiri
na biyu.
Ya
ce Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da kwasa-kwasan Digiri 12
ga Kwalejin inda ya nuna cewa dukkan kwasa-kwasan na karkashin kulawar Jami’ar
Ahmadu Bello ta Zariya da Jami’ar Bayero ta Kano.
"Kwalejin
na da dukkan kayan aiki a sashen Faransanci amma matsalar shi ne rashin malamai,"
in ji shugaban Kwalejin.
Ya
kuma roki Ministan da ya shiga gaba wajen kulla alaka a tsakanin kwalejin
Jamhuriyar Nijar ta fuskacin horar da ma’aikata da bunkasawa tare da kuma
shirin musayar dalibai.
A
nasa jawabin, Ministan ya yi alkawarin shirin gwamnatin Jamhuriyar Nijar na
hada kai da gwamnatin jihar Kano a fannin shirin musayar dalibai, horar da
ma’aikata da kuma ci gaba.
Ita
ma a nata jawabin, kwamishiniyar ilimi ta jihar Kano, Dakta Mariya Bunkure, ta
bada tabbacin cewa kwalejin gwamnatin jihar zai bayar da goyon baya ga wannan
hadin gwiwar.
No comments