Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gidauniyar Hassan Rilwan Ta Bai Wa Mata 20 Tallafin Miliyan Daya

Daga Idris Umar Kaduna Gidauniyar Seed Capital Revolving Fund mallakar Alhaji Hassan Rilwan babban Sakatare a hukumar bayar da t...


Daga Idris Umar Kaduna

Gidauniyar Seed Capital Revolving Fund mallakar Alhaji Hassan Rilwan babban Sakatare a hukumar bayar da tallafin ilmi na jihar Kaduna. Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen watsa labarai da suka halarci wannan taro.

An gudanar da taron ne a babban dakin taro na Sakateriyar Jam'iyyar APC na karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna. Shugabanin Jam'iyyar ta APC da manyan 'yan siyasa maza da mata ne suka halacci wajen taron.

Kamar yadda gidauniyar ta shelanta a wajen taron cewa, mata 20 ne za su sami tallafin kuma kowacce dubu hamsin za a bata.

Bayan sauraren wasu mata masu yawa ne da suka nuna jindadin su da tallafin da suka samu a lokutan baya da wannan gidauniyyar ta ba su sai aka ci gaba da sauraren jawabin sanya albarka ga shugaban gidauniyar Alhaji Hassan Rilwan.

Abin ban sha'awa da ya faru a wajen taron shi ne, baki na gama jawabi sai alat ya dinga shigowa lalitar wadda za a ba tallafin. Bisa haka ne wurin ya dauki tafi da jinjina ga wannan gidauniyar.

Shugaban mata na Jam'iyyar APC da Malama Maryam Shaibu ne suka yi jawabi a madadin sauran mata da suka sami wannan tallafi na baya da na yanzu naira dubu 50 ga kowace mace. Ta ce da ikon Allah sai Allah ya biya mashi bukatarsa.

Karshe ta yi kira ga sauran masu rike da madafun iko da su yi koyi da Alhaji Hassan Rilwan wajen tausayi da taimako.

Bayan an kammala taron ne sai wakilinmu ya zanta da shugaban gidauniyar inda ya baiyana dalilin da yasa gidauniyar ta bada tallafin ga mata a wannan lokacin.

Farko ya ce, bayar da taimako ga mai bukata ibada ne, Allah na farinciki da hakan. Na biyu ya ce wajibi mu tallafawa mata bisa gudummawar da suka bayar wajen tabbatuwar wannan gwamnati mai albarka ta APC a jihar Kaduna da kasa baki daya.

Ya ce bisa haka ne yasa suka fitar da tsari na ba su tallafin Naira dubu 50 su yi sana'a amma kowanne sati za su saka Naira dubu daya (N1, 000) a wani asusu wanda a shekar za su tara fiye da abin da aka ba su sai kuma a ba wasu kuma da haka ne tallafin zai isa wurare da dama a fadin mazabun da muke da su a karamar Hukumar Sabon Gari.

Kuma ya yi kira ga matasa su zauna kafiya yayin gudanar da zabukan dake tunkaromu nan gaba tare da karfafa su da su nemi ilmi. 

Taron ya sami halartar Sakataren karamar hukumar Sabon Gari da shugaban Jam'iyyar APC da mataimakinsa Alhaji Uwaisu da Alhaji Hamisu Jarma da sauran manyan 'yan siyasa na karamar hukumar ta Sabon Garin kuma dukkansu sun yi jawabi mai kyau tare da fatan alheri ga taron.

 An yi taro lafiya an tashi lafiya .

No comments