Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Tubabbun Ƴan Daba 152 Da Tallafin Naira Miliyan N100

A yau Juma'a dai wasu gungun matasa, su 152, waɗanda su ka yi adabo da dabanci, sun kasance baki har kunne, bayan da Gwamnan...


A yau Juma'a dai wasu gungun matasa, su 152, waɗanda su ka yi adabo da dabanci, sun kasance baki har kunne, bayan da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya raba musu tallafin Naira Miliyan Ɗari, (N100 million) sakamakon tuba da su ka yi da daba.

Zulum, wanda ya raba tallafin a Maiduguri, bayan da waɗanda su ka amfana ɗin sun kammala horo a kan kasuwanci na tsawon wata ɗaya.

Ya ce an raba musu kuɗin ne domin su yi jari domin su dogara da kansu su kuma bada gudunmawa wajen ci gaban jihar.

A cewar sa, 16 da ga cikin matasan za su samu Naira Miliyan 2 kowannen su, bayan da sauran 136 kuma kowanne su zai karɓi Naira Dubu 500.

Zulum ya ƙara da cewa waɗanda su ka amfana ɗin za su biya rabin kuɗin da a ka basu a shekara uku.

Gwamnan ya kuma sanar da cewa zai ɗauki nauyin karatun ɗa ɗaya da ga cikin ƴaƴan matasan kowannen su.

Ya ƙara da cewa sun kwashe shekaru da dama suna dabanci amma ba abinda su ka tsinana, inda ya ce in dai su ka rike wannan tallafin da zuciya ɗaya to za su samu ci gaba sosai a rayuwarsu.

No comments