Kimanin hukumomin gwamnati da kamfanoni 42 mallakar gwamnatin Nijeriya, kasar za ta cefanar a wannan shekarar in ji hukumar kula...
Kimanin hukumomin gwamnati da kamfanoni 42 mallakar gwamnatin Nijeriya, kasar za ta cefanar a wannan shekarar in ji hukumar kula da kamfanonin gwamnati.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Juma'a ta ce an amince da duka hada-hadar da Majalisar kasar kan sayar da kamfanonin gwamnati ta gabatar, wadda mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo ke jagoranta.
"Za a yi cinikayyar kamfanonin makamashi 11, da kuma 10 daga bangaren masana’antu da aikace-aikace, sai guda takwai daga bangaren noma da aikace-aikacen cikin gida, sai kuma 13 a bangaren ayyukan more rayuwa da kanwace tsakanin gwamnati da kamfanonin mutane masu zaman kansu," in ji nasarwar.
An fara samun batun ne daga zaman majalisar na farko a wannan shekara da aka yi a fadar gwamnati bayan kaddamar da shi da aka yi a makon jiya.
No comments