Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya, ta mika takardar shedar shugabancin jam’iyyar ga bangaren gwamnan jihar Kano, wan...
Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya, ta mika takardar shedar shugabancin jam’iyyar ga bangaren gwamnan jihar Kano, wanda ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin sabon shugaba.
A dazun nan ne Sakataren rikon jam’iyyar na kasa Mista John Akpanudoedehe, ya mika takardar ga Abdullahi Abbas, wanda yake tare da Gwamna Ganduje da dan Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa da Kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sulen Garo.
Bayar da takardar shedar ta biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta kasar ta yi ne inda ta soke hukuncin babbar kotun da a baya ta ba bangaren tsohon gwamnan jihar Mallam Ibrahim Shekarau nasara a shari’ar shugabancin.
Ɓangaren Shekarau din wanda ke da Ahmadu Haruna Zago a matsayin shugaban jami’iyyar ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun da ya ce shugabancin ɓangaren gwamna ne halastacce.
Ahmadu Haruna Zago, ya faɗa wa BBC Hausa cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su ɗaukaka ƙara.
"Za mu ɗaukaka ƙara mana, ai bin umarnin daban kuma ɗaukaka ƙara daban," in ji shi. "Lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun."
Hakan na nufin Kotun Ƙoli ce za ta raba gardama idan suka ɗaukaka ƙarar, kasancewar Kotun Ɗaukaka Ƙara ce ta yi hukuncin na yanzu.
A zaman da ta yi yau Alhamis a Abuja, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce - ba na Haruna Zago ba.
A makon da ya gabata ne bangaren Shekarau ya yi watsi da wani yunƙurin sulhu da jam'iyyar ta ƙasa ta yi, inda ta naɗa Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamatin sasanta rikicin da suke yi.
No comments