Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Honorabul Isa Hazo A Mahangarmu -Prince Muktar

Daga Idris Umar, Zariya Yau tabaranmu zai hasko mana wainar da ake toyawa a Gundumar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari ne t...


Daga Idris Umar, Zariya

Yau tabaranmu zai hasko mana wainar da ake toyawa a Gundumar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari ne ta jihar Kaduna.

Bisa haka ne muka aike da tambayar mu akan fitaccen Dan siyasar nan da ake kira Kenze wato Dan majalisar jiha mai wakiltar Gundumar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari ga daya daga cikin masoyansa kuma mai taimaka mashi a bangarori da dama a siyasance a halin yanzu wato Sir Prince Muktar. 

Tambayarmu ko ita ce ina Honorabul Muntari Isa Hazo yake ne?

Sir Prince Muktar sai ya amsa tambayar tamu kai tsaye ga wakilinmu kamar haka; Prince ya ce, Honorabul Muktar Isa Hazo yana nan a kujerarsa na Dan majalisa mai wakiltar Gundumar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Prince ya kara da cewa duk da cewa wasu na yi wa kujerar ta sa mummunan fassara da ya kamata a bani dama in yi karin haske akan lamarin. Prince ya ce, da yawan mutane suna zaton dan majalisa shi ke da damar yin aiki ga jama'arsa kamar su tituna da kwalbatoci wanda ba haka lamarin yake ba.

Prince ya ce, shi fa aikin Dan majalisa shi ne, ya samawa jama'arsa doka da za ta kawo ci gaban yankinsa da zarar an yi bincike akan kudirin na sa ya yi daidai da dokar kasa to sai a sanya mata hannu don aiwatar da ita.

Bisa haka ne Prince ya yi roko ga jama'ar Gundumar Basawa dake karamar hukumar Sabon Gari da cewa su yi hakuri akwai kyakkyawar manufa a zuciyar Honorabul Hazo ga jama'arsa.

Matashin ya kara da cewa da yardar Allah Honorabul Hazo zai isar da dukkan koken jama'arsa ga majalisa tare da bin sawu kafa da kafa. Amma kuma ya yi rokon dukkan wanda tafiyar Honorabul Hazo ta batawa rai to ya yi hakuri rashin fahimta ce kawai amma da ikon Allah komai zai tafi daidai.

Karshe ya yi kira ga matasa da su zama wakilai na gari kar su bari wani Dan siyasa ya yi amfani da su wajen tayar da hankali. Ya ce tayar da hankali ba abin yi bane ga matasa hadin kai da son juna shi ne abin da ya dace a garemu baki daya.

Tuni ya ce hanya a bude take ga duk mai son bayar da shawara gare su  kuma ya yi fatan Alheri ga dukkan matasan karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya.

Zuwa hada wannan rahoto namu bincike ya tabbatar da cewa jama'ar Gundumar Basawa dake karamar hukumar Sabon Garin na nuna soyayya ga shi Honorabul Isa Hazo duk da cewa wasu na nuna turjiya akan lamarin soyayyar nasa.

Haka ne yasa wasu ke ganin cewa ko da Hazo zai kara fitowa takara to akwai cakwakiya a gabansa amma da yake Hazo mutum ne mai biyayya zai iya samun nasara in dai ya yi amfani da wancan bai wa da Allah ya ba shi.

No comments