Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Jami'o'in Ƙasar Ukraine Sun Kulla Yarjejeniya Da MAAUN Kano Kan Bincike Da Tallafin Ilimi

Daga Ali Kakaki Jami’o’in kasar Ukraine guda biyu, Jami'ar V.N Karazin Kharkiv ta Kasa da kuma Jami’ar Harkokin Kasuwanci da...

Daga Ali Kakaki

Jami’o’in kasar Ukraine guda biyu, Jami'ar V.N Karazin Kharkiv ta Kasa da kuma Jami’ar Harkokin Kasuwanci da Doka ta Lviv, sun bayyana aniyarsu ta kulla alaka da Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya dake Kano a fannin bincike da sauran shirye-shiryen shiga tsakani na tallafin ilimi.


Wani memba na tawagar Ukraine, Farfesa Valeriy Reznikov na Jami'ar V.N. Karazin Kharkiv ta kasa ne ya bayyana hakan a lokacin da suka kai ziyarar aiki a Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya da ke Kano a ranar Alhamis.

Tawagar ta isa Kano ne domin duba da tantance shirye-shiryen Jami'ar na MAAUN din kan shirinsu na kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da jami’o’insu.

Ya bayyana cewa rattaba hannu kan yarjejeniyar zai taimaka wajen kawo ci gaban ba da ilimi mai inganci wanda ya dace da duniya ta hanyar amfani da fasahar zamani. 

A cewarsa, haɗin gwiwar da MAAUN zai bayar da damar gudanar da wasu kwasa-kwasan a fannin kimiyyar likitanci, Tsaro da aminci, kiɗa da nishaɗi, kasuwanci, al'adu da noma da dai sauransu.

Ya kuma bayyana cewa hadin guiwar har wala yau zai bai wa dalibai daga Jami'ar damar gudanar da wasu darussa a Jami'o'in Ukraine, kazalika ma takwarorinsu daga Jami'o'in Karazin da Lviv za su zo MAAUN domin gudanar da bincike na ilimi.

Ya kuma bayyana cewa Jami'ar VN Karazin Kharkiv ta Kasa na daya daga cikin tsofaffi kuma mafi girma a Turai, wanda aka kafa a shekarar 1804, inda ya kara da cewa sun zo ne tare da wakiliyar Jami'ar kasuwanci da shari'a ta Lviv, Misis Olgar Krasnopera, domin ganawa da takwarorinsu na MAAUN, domin lalubo hanyoyin da za su hada kai wajen gina alakar ilimi da tattalin arziki da Nijeriya ta hanyar Jami’ar ta Kano.

Wakili a tawagar kuma wakilin jami'o'in kasar biyu ta hanyar shirin Cibiyar fasahar horaswa da dogaro da kai ta FTAISA, Dr. Cliff Ogbede ya tabbatar cewa manyan Malamai masana daga Jamus, Poland da sauran kasashen Turai za su ziyarci MAAUN a Kano, domin gabatar da laccoci da bayar da taimakon bincike.

Ogbede ya kara da cewa, hadin gwiwar zai kuma bai wa Jami'o'in da suka yi hadin gwiwar daga kasar Ukraine damar gudanar da shirye-shiryensu na cikin gida da kuma bayar da kwasa-kwasan da za su taimaka wajen gina sabbin ‘yan kasuwa domin bunkasar tattalin arzikin ƙasashen.

PHe ya ce Jami'o'in da suka yi hadin gwiwar za su gudanar da wani shiri da ya kira shirin musayar ilimi na '2 da 2,' inda zababbun daliban Jami’ar Maryam Abacha American University za su shafe shekaru biyu a Nijeriya sannan su wuce kasar Ukraine su kara shekaru biyu domin samun shaidar takardar digiri a Ukraine.

Ya ce ma'aikatan Jami'ar MAAUN ne za su gudanar da wani bangare na tsarin karatun digirin a yayin da malaman Ukrainian za su kammala jadawalin karatun.
 
Ogbede ya bayyana cewa Jami'o'in Ukraine za su tallafa wa MAAUN a bangaren bincike, taron karawa juna sani da kuma taron karawa juna sani na kasa da kasa, baya ga taimaka wa malamanta su buga kasidu masu tasiri a cikin mujallun kasashen Yamma.

Ya ce bisa la’akari da kalubalen tsaro na duniya da ake fuskanta da ya yi wa kasar illa, jami’o’in hadin gwiwa na kasar Ukraine za su taimaka wa MAAUN wajen samar da cibiyar nazarin harkokin tsaro a harabar jami’ar, wadda za ta taimaka wa gwamnatin Nijeriya a fannin bincike da tsare-tsare.

A na ta bayanin, Misis Inna Kolomyichuk, wacce ita ce Daraktar Cibiyar Ilimin Yukren-Afirka ta Jami'ar V.N. Karazin Kharki ta kasa, ta bayyana gamsuwarta kan yadda Jami’ar Maryam Abacha American University ta shirya tsaf domin kulla yarjejeniya da jami’arta.

Misis Kolomyichuk ta bayyana cewa irin wannan hadin gwiwar zai ba da ilimi mai nagarta ta hanyar amfani da fasahar zamani. 

Ta ba da tabbacin shirin jami’arta na kulla alakar da za a ci moriyar juna tsakanin su da MAAUN domin bayar da kwasa-kwasan na musamman kamar su kwarewa a bangaren kasuwanci da dogaro da kai, karatun digiri na daya da na biyu da dai sauransu.

Ta kuma gayyaci mahukumtan Jami'ar da su ziyarci jami'arta da ke Ukraine domin duba wuraren koyo mai inganci da ya dace da duniya da kuma cibiyoyin bincike.

Memba a tawagar kuma wakilin kasar na jami'o'i biyu ta hanyar shirin Cibiyar horas da fasaha da ci gaban kasuwanci na FTAISA ya nuna cewa haɗin gwiwar tare da Jami'o'in Ukraine zai mayar da hankali wajen daga darajar matsayin ilimi a kasar, tun da masana daga Ukraine sun kasance a cikin ƙungiyoyin shahararrun cibiyoyin ilimi a ƙasarsu.

A na shi bayanin shugaba kuma wanda ya kafa Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya kaddamar da tawagar jami’o’in kasar Ukraine da suka taho tun daga kasar Ukraine har zuwa jami’ar MAAUN da ke Kano domin tantance jami’ar.

Ya yi alkawarin kammala sauran bukatun da za su kai ga cin moriyar shirye-shiryen kulla alakar  mai amfani ga dukkanin Jami'o'in.
 
"Wannan haɗin gwiwar an yi ta ne da niyyar  gina alaka mai ƙarfi da haɗin gwiwa tare da jami'o'in Ukraine wanda zai ba wa ɗalibanmu damar samun ilimi tare da dabarun da za su sa su sami aiki da kuma samar da ayyukan yi a duniya," in ji shi.

No comments