Daga Muhammad Farouk Jam’iyyar PRP ta tabbatar da matashin nan, Aliyu Samba a matsayin wanda zai jagoranci shugabancin jam’iyy...
Daga Muhammad Farouk
Jam’iyyar PRP ta tabbatar da matashin nan, Aliyu Samba a matsayin
wanda zai jagoranci shugabancin jam’iyyar a jihar Kano. Bayanin hakan na kumshe
ne a sanarwar da Hedikwatar jam’iyyar PRP ta kasa ta fitar, wanda shugabanta na
kasa, Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ya sanyawa hannu ya kuma fitar a yau
Litinin.
Sanarwar wacce aka yi wa take da; ‘Shugaban Jam’iyyar PRP Ya
Tabbatar Da Samba A Matsayin Zababben Shugaban Jam’iyyar PRP A Jihar Kano’, ta
jaddada cewa ba ta san wani shugaban jam’iyyar a jihar Kano ba da ya wuce Aliyu
Samba. Inda sanarwar ta ce; “Wannan na tabbatar da cewa Malam Aliyu Samba shi ne
zababben shugaban jam'iyyar PRP a jihar Kano. An zabi Malam Samba da gagarumin rinjaye
ne a taron jam’iyyar da aka gudanar a Kano a ranar Asabar 12 ga Fabarairu, 2022”,
in ji sanarwar.
Ta ci gaba da cewa; “A iya saninmu babu wani mai suna Injiniya Abba
Namatazu a taron majalisar jihar da aka yi a ranar Asabar 12 ga watan Fabrairun
2022, wanda ya samu halartar wakilai daga kananan hukumomi 44 na jihar Kano, kashi
uku daga cikinsu mata ne; da kuma masu sanya ido a zaben daga Hukumomin zartarwa
na tarayya.
“Tuni Injiniya Namatazu da shugabansa Malam Falalu Bello aka sauke
su daga mukamansu na shugabancin jam’iyyar a matakin jiha da kasa baki daya.
Zaben Samba a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Kano ya sake tabbatar da
rashin shugabancin Namatazu da Falalu Bello a jam’iyyar PRP.
“PRP jam'iyya ce mai bin tafarkin dimokuradiyya wacce ba ta amince
da zaman dirshan, na kashin kai ko kuma na son rai ba. Da zarar wa’adin shugaba
ya kare, sai a maye gurbinsa da halastaccen zabin jama’a.
“Shugabancin tsofaffi a cikin jam'iyyar wadanda ke adawa da nagartattun
matasa da mata da ke taka rawar gani a PRP, sun fi dacewa su tsara tare da
daidaita al'amuran dimokuradiyya a cikin jam'iyyar: jama'a suna yanke zabin
kansu ne bisa doka, tsarin mulkin jam'iyyar, sannan da kuma, fiye da komai,
kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya (na shekarar 1999 da aka yi wa
kwaskwarima), ba wai son rai irin na Falalu Bello ko siyasar dan bangansa,
Namatazu ba”, suka tabbatar.
Har wala yau sanarwar ta kara da cewa; “Jam’iyyar PRP a bude take ga duk ‘yan Nijeriya, matasa da Dattawa, mace da namiji, ba tare da la’akari da yanki, kabila, addini, ko akida ba. Abin da muka mayar da hankali a kai shi ne mutunta dokokin kasa da kuma jigon ka’idojin jam’iyya”.
Sun karkare da cewa; “Ina kira ga kafatanin ‘yan Nijeriya masu
kishin kasa, masu mutunta ‘yan adamtaka, ‘yan kishin kasa, ‘yan gurguzu, ‘yan
kasuwa masu son kawo ci gaba, matasa, da shahararrun kungiyoyi da su shiga jam’iyyar
PRP a yau a fafutukar sake gina siyasa a Nijeriya a matsayin sana’ar yi wa al’umma
hidima ba son zuciya ba.”
No comments