Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kabilu Mazauna Jihar Zamfara Sun Tabbatar Da Goyan Bayansu Ga Gwamna Matawalle

Daga Hussaini Ibrahim Tawagar shugabanni Kabilun mazauna cikin Jihar Zamfara, sun jaddada goyan bayansu ga gwamna Bello Matawall...


Daga Hussaini Ibrahim

Tawagar shugabanni Kabilun mazauna cikin Jihar Zamfara, sun jaddada goyan bayansu ga gwamna Bello Matawalle ga sabon mai bai wa Gwamnan Matawalle shawara a hukumar da al'umma, Honorabul Aliyu Suleman Dansadau.

Tawagar shugabanin al'ummar da ba 'yan asalin jihar ba, karkashin jagorancin Shugabansu na Jihar, Injiniya Joel Thomas, sun ziyarci sabon mai bai wa gwamna Matawalle shawara ne, Honorabul Aliyu Suleman Dansadau domin jaddada goyan bayansu ga Gwamnatin jihar da kuma taya shi murnar zamowa mai bai wa gwamna Matawalle shawara a hukumar.

Shugaban Joel Thomas, ya bayyana cewa, gwamna Matawalle ya sanya wanda ya dace akan jagorancin hukumar kuma muna mai tabbatar muku da cewa, zamu baka goyan baya da kuma hadin kai wajen ci gaban wannan ma'aikata tamu, inji Joel Thomas.

Jole ya kuma tabbatar da cewa, Gwamnatin jihar Zamfara na ba su hakkokinsu yadda ya kamata ba tare da nuna bambanci ba wajen bada tallafi; "tana daukar mu tamkar 'yan jihar muna godiya akan haka", inji shugaba Jole.

A jawabin mai ba gwamna Matawalle shawara a hukumar, Honorabul Aliyu Suleman Dansadau ya tabbatar masu da cewa, gwamna Matawalle na kowanne kuma baya nuna bambancin al'umma ko yare, indai mutum yana cikin jihar Zamfara daidai yake ga kowa da kowa, inji Hon. Dansadau.

Hon. Aliyu Dansadau ya kuma tabbatar masu da cewa, Ofishinsa a bude yake ga kowa da kowa dan amsar shawara da koken akan abin da ya shafi al'ummar da ba 'yan asalin jihar ba.

Kuma Gwamnatin jihar Zamfara za ta samar wa al'ummar da ba 'yan asalin jihar ba dawwamammen zaman lafiya wanda dama yawancinsu 'yan kasuwa ne, sakamakon magance matsalar tsaro yanzu haka kasuwanin da ba sa ci yanzu ana hada-hada kuma babu irin al'ummar da ba ta zuwa cikin kasuwar, wannan babbar nasara ce a garemu, a cewarsa. 

A karshe Daraktan hukumar, Kabiru Muhammad Maradun ya bayyana godiyarsa ga tawagar Shugabannin al'ummar jihar Zamfara akan jaddada goyan bayan gwamnatin gwamna Matawalle. 

Kabiru Maradun ya kuma tabbatar da cewa, duk wani tallafi ko taimakon da gwamnatin ke badawa al'ummar da ba 'yan asalin jihar na cin gajiyarsa a wannan Ma'aikata, dan haka ma insha Allah yadda aka saba haka zai dore tunda ga sabon mai ba wa gwamnan Matawalle shawara a hukumar, Hon. Aliyu Suleman Dansadau ya shigo wannan Ma'aikata kowa zai dara da yarda Allah.

No comments