Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kashi 31 Cikin 100 Na Malaman Borno Ne Kawai Kwararru - Rahoto

  Kwamitin da gwamnatin Borno ta kafa domin tantance kwarewar malaman makarantu a matakan kananan hukumomi, ya ce kashi 31 cikin 100 na mala...

 


Kwamitin da gwamnatin Borno ta kafa domin tantance kwarewar malaman makarantu a matakan kananan hukumomi, ya ce kashi 31 cikin 100 na malaman jihar ne kawai suka cancanci aikin.

Kwamishinan ilimi a jihar ta Borno Lawan Wakilbe ne ya gabatar da rahoton tantance malaman ga gwamna Babagana Umara Zulum ranar Alhamis a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

Tun da fari gwamnan na Borno ya dorawa kwamitin aikin tantance jumillar malaman makarantun dubu 17 da 229 a kananan hukumomi 27 na jihar, inda aka yi musu jarabawar tantancewar a watan Janairun 2022.

Matsalar rashin kwarewar malamai ba sabuwa ba ce a Najeriya, inda a shekarun baya aka rika fitar da rahotanni kan koma bayan da ilimi ke fuskanta a kasar dalilin matsalar ta karancin kwararrun malamai, abinda masana ke dangantawa da rashin daukar mutanen da suka cancanta domin gudanar da aikin, da kuma matsalar alfarma da ta rashawa, sai kuma rashin tsarin albashi mai kyau da zai ja hankalin zakakuran matasa wajen rungumar aikin na koyarwa.

No comments