Marigayi Janaral Aminu Maude Hukumar EFCC a ranar Litinin sha hudu ga watan Fabarairu, 2022 ta samu nasarar karbe wasu ...
Marigayi Janaral Aminu Maude
Hukumar EFCC a ranar Litinin sha hudu ga watan Fabarairu, 2022 ta samu nasarar karbe wasu kadarori guda ashirin da kudin su ya kai Naira biliyan goma da miliyan dari tara da talatin da biyar na wani babban jami’in soja amma wanda wasu ke kula masa da su da suka hada da Marigayi Janar Aminu Maude da wasu kamfanonin kamar Atlasfield integrated Services Nigeria Limited, Marhaba Events Place, Aflac Plastics da Atlasfield Gas Plant Limited.
Mai shari’a N. E Maha na babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ne ya bayar da umarnin inda ya yanke hukuncin bukatar haka daga lauyan EFCC Cosmos Ugwu da Musa Isah.
A shekarar 2020 kotun ta umarci karbe kadarorin na wucin gadi biyo bayan bukatar haka da masu shigar da kara suka yi inda suka yi zargin an samu kadarorin ne ta hanyar haram.
Sai kuma a ranar Litinin kotun ta bayar da umarnin karbe kadarorin gaba daya.
Kadarorin dai suna garuruwan Kano, Katsina, Calabar da Kaduna da kudin su ya kai Naira biliyan goma da miliyan dari tara da talatin da biyar, kuma sun hada da gidan mai, wuraren taro, kasuwannin zamani da aka fi sani da Plaza, sai kamfanin hada bulo da na yin robobi da na ruwan sha da sauransu.
Ga hotunan wasu kadarorin da EFCC ta saki;
No comments