Kotu Ta Kori Karar Sauya Shekar Gwamnan Zamfara Zuwa APC


 Daga Hussaini Ibrahim

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau a jihar Zamfara ta kori karar da ke kalubalantar sauya shekar Gwamna Bello Matawalle, zuwa jam'iyyar APC daga Jamiyyar PDP.

Kotun ta kuma bayar da umarnin biyan wadanda ake kara naira miliyan 1 da masu shigar da kara su biya kowane daya daga cikin wadanda ake kara saboda bata masu lokacin da su ka yi na zuwa kotun.

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Aminu Bappah Aliyu, ya ce kotun ba ta da hurumin sauraren karar. Mai shari’a Bappa, ya ce asalin koken da masu shigar da kara suka shigar ba shi da wani inganci.

Ya kuma kara da cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba kowane mutum damar shiga kowace Jam'iyyar da ya ke bukata. Don haka canza shekar gwamna Matawalle zuwa wata Jam'iyyar zai tafi da mukamin da yake akai.

Mai Sharia Aliyu ya ce, 'yan majalisar dokokin jihar ne kadai ke iya korar gwamna a bisa mukaminsa.

Post a Comment

0 Comments