Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kwankwaso Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Ƙungiyar Siyasa A Nijeriya

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jagorantar wani gagrumin taro na wasu manyan siyasar Nijeriya karkashin wani yunkuri mai suna The...


Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jagorantar wani gagrumin taro na wasu manyan siyasar Nijeriya karkashin wani yunkuri mai suna The National Movement TNM.

Fitattun mutane da ƴan siyasa da suka halarcitaron sun haɗa da Alhaji Tanko Yakasai da Capt Idris Wadatsohon gwamnan Kogi da Rufai Alkali da Aminu Ibrahim Ringim tsohon dan takarar gwamna a jihar Jigawa da kuma Inijiniya Buba Galadima.

A jawabin Kwankwaso ya ce wasu ƴan Najeriya ne da suka damu da abin da ke faruwar suka haɗa kai don ceto ƙasar daga mawuyacin halin da ta shiga.

Ya ce yunƙuri ne na ƴan Nijeriya masu kishi da suke zaune a gida da kasashen waje.

A cewarsa za su duƙufa wajen farfaɗo da tattalin arzikin kasar da inganta rayuwar ƴan kasa a birni da karkara

Ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar matsalar tsaro da ta addabi Nijeriya.

No comments