Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Lauyoyin Sanata Marafa Sun Gamu Da Fushin 'Yan Bangar Siyasa A Kotu

Daga Hussaini Ibrahim Lauyoyi masu kare bangaren Jam'iyyar APC na Sanata Kabiru Garba Marafa, sun gamu da fushin 'yan ba...


Daga Hussaini Ibrahim

Lauyoyi masu kare bangaren Jam'iyyar APC na Sanata Kabiru Garba Marafa, sun gamu da fushin 'yan bangar siyasa da, tare da Sakataren yada Labarai na bangaren Sanata Marafa, sakamakon harin 'yan bangar siyasa jim kadan bayan kammala zaman kotun majistiri ta bakwai a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Jami'in yada labarai na Jam'iyar APC, Bangaren Sanata Kabiru Marafa, Bello Bakyasuwa ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manaima labarai a Gusau.

Bakyasuwa ya kara da cewa, kamar yadda aka sani zaman kotun a jiya wanda bangaren Sanata Kabiru Marafa ya shigar yana kalubalantar Jam'iyyar APC ta kasa kan laifuffuka daban-daban.

"Bayan kammala zaman kotun sai wasu 'yan bangar siyasa, suka farmake mu da duka a kokarina na shiga motar lauyanmu ne wasu su kai ta dukan motar bada san ransu ba Allah ya kubutar da mu", inji Bakyasuwa. 

"Shi kuwa daya Lauyan namu sai da ya yi garkuwa da Kwamishinan shari'a na Jihar Zamfara sannan ya samu kubuta. Wannan ta'addanci bai bamu mamaki ba, saboda tun kafin lokacin wasu sun kira ni suka kuma gargade ni ka da na kuskura ya halarci zaman kotun na jiya, amma na ki bin umarni su da barazanarsu", inji shi. 

Bakyasuwa ya ce kara da cewa, abin da  ya fi ba su mamaki shi ne yadda za a ce a cikin harabar kotu a yi wannan ta'addanci wanda a gaban kowa jami'an tsaro da 'yan jarida, ya ce idan in har aka ce ba ka da aminci a gidanka ba ka da shi a kotu to babu inda za ka same shi.

Bakyasuwa ya yi kira ga jami'an tsaro da babbar murya akan su dauki mataki akan wadannan 'yan ta'adda dan ba za su hana mu zuwa kotu ba wajen neman hakkinmu dan haka kare mu a wajen su ya zama wajibi idan ko ba su iya kare mu, to lallai mu zamu kare kan mu, inji Sakataren yada Labaran na Jam'iyyar APC bangaren Sanata Kabiru Marafa. 

No comments