BBC ta labarto cewa ma’aikatan Nagarta Rediyo da ke Kaduna sun rufe tashar sakamakon abin da suka kira rashin biyansu albashi na tsawon wata biyar.
Ma’aikatan sun fito suna zanga-zanga domin neman haƙƙinsu tare da nuna adawa da shugabanninin gidan rediyon.
Tashar rediyon mallakin Janar Aliyu Gusau ce da ke a matsakaicin zango. Ma’aikatan sun yi kiran da a diba bukatunsu.
0 Comments