Hukumar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), da Franco-British International University (FBIU), ta Kad...
Hukumar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya (MAAUN), da Franco-British International University (FBIU), ta Kaduna, sun mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalai, Majalisar Sarkin Musulmi da Gwamnatin Jihar Sakkwato, bisa rasuwar Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Danbaba.
Danbaba, wanda ya rike sarautar Magajin Garin Sakkwato, ya rasu ne a ranar Asabar 12 ga watan Fabarairun, 2022 yana da shekaru 50 a gidansa da ke Kaduna sakamakon gajeruwar rashin lafiya.
Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da wanda ya kafa kuma shugaban Jami’ar Maryam American University, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya raba wa manema labarai a Kano a ranar Talata.
A cewar sanarwar, rasuwar Sarkin gargajiyar babban rashi ne ba ga iyalansa da Majalisar Sarkin Musulmi da jihar Sakkwato kadai ba, har ma da kasa baki daya.
"Na yi matukar kaduwa da samun labarin rasuwar Alhaji Hassan Danbaba, Magajin Garin Sakkwato. Allah Ta'ala ya gafarta masa kurakuransa, ya sanya shi a Aljannah Firdausi.
Ya bayyana marigayin a matsayin Mai sarautar gargajiya mai mutunci kuma kamilin mutumi wanda ya ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban daular Sakkwato da ma Nijeriya baki daya.
"A madadin Hukumar Gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, Majalisar Sarkin Musulmi, gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato tare da addu’ar Allah madaukakin Sarki ya sanya shi a Aljannah Firdausi, ya kuma bai wa iyalansa haÆ™urin jure rashinsa."
“Shugaba kuma wanda ya samar da Jami'ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a madadin hukumar gudanarwa yana kuma mika ta’aziyyarsa ga daukacin al’ummar jihar Sakkwato kan wannan babban rashi,” in ji sanarwar.
Marigayin ya bar mata uku da ‘ya’ya shida, tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a Sakkwato.
Allah ya jikansa da Rahama yasa ya huta, amin.
TALLAR JAMI'AR MAAUN
No comments