Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, (MAAUN) dake Kano, ta sanyawa wani titi a jami’ar sunan ministan...
Hukumar gudanarwar Jami’ar Maryam Abacha American University ta Nijeriya, (MAAUN) dake Kano, ta sanyawa wani titi a jami’ar sunan ministan ilimi mai zurfi da binciken kimiyya na Jamhuriyar Nijar, Dr. Mamoudou Djiboh.
Da yake jawabi jim kadan bayan kaddamar da hanyar, shugaba kuma wanda ya kafa Jami’ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce sun yanke shawarar karrama Ministan ne saboda jajircewarsa da sadaukarwarsa wajen bunkasa fannin ilimi musamman a Jamhuriyar Nijar da ma nahiyar Afirka baki daya.
Taron wanda ya gudana a ranar Laraba, 16 ga watan Fabrairu, ya samu halartar Kwamishiniyar ilimi ta jihar Kano, Dakta Mariya Bunkure da kuma manyan ma’aikatan jami’ar MAAUN.
"Mun yanke shawarar karrama Ministan ne ta hanyar sanya wa hanyar sunan shi saboda jajircewa da sadaukarwa wajen ganin al'ummar Nijar da ma daukacin nahiyar Afirka sun samu ilimi," in ji Farfesa Gwarzo.
Da yake jawabi a wajen taron, Ministan, Dokta Mamoudou Djiboh ya gode wa Farfesa Gwarzo da Hukumar Kula da Jami’ar bisa wannan karramawar.
Ya kuma yabawa shugaba kuma wanda ya assasa Jami’ar MAAUN, Farfesa Gwarzo bisa kafa jami’ar da kuma samar mata da kayyayakin zamani da fasaha.
Ya ce ziyarar da ya kawo Nijeriya na da alaka da samar da alaka tare da hadin gwiwa a tsakanin jami’o’in Jamhuriyar Nijar da na Nijeriya domin bunkasa ilimi a kasashen biyu.
Dokta Djiboh ya bayyana fatan cewa ziyarar da ya kawo Jami’ar Maryam Abacha American University da ke Nijeriya a Kano da sauran jami’o’in jiha da kwalejojin ilimi na jihohin Kano da Katsina, za ta ci gaba da samar da hadin gwiwa musamman ta fuskar horar da malamai da kuma musayar dalibai a wasu darussan.
Bugu da kari, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci a kara ba da hadin kai ta hanyar karfafa shirye-shiryen musayar dalibai da sauran batutuwan da suka shafi hadin gwiwa tsakanin manyan makarantun Jamhuriyar Nijar da jihar Kano.
Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce jihar Kano a shirye take ta hada kai da jamhuriyar Nijar a fannonin da suka dace da kuma wacce za ta ci moriya. Ya godewa tawagar daga jamhuriyar Nijar bisa ziyarar tare da bada tabbacin hadin kai.
A nasa jawabin, Ministan ya ce shekaru da dama da suka gabata dalibai daga jamhuriyar Nijar sun kasance suna zuwa Nijeriya musamman Kano domin yin karatu a manyan makarantu daban-daban; “Yanzu muna son a farfado da shirin musayar dalibai ya kuma dore.
“Ta hanyar haÉ—in gwiwar za mu bunkasa ingantacciyar ilimi da bincike a manyan makarantunmu waÉ—anda za su amfanar da mu duka,” inji shi.
Ministan wanda ya kai irin wannan ziyarar a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST) da ke Wudil, yana tare ne da rakiyar kwamishiniyar ilimi mai zurfi ta Jihar Kano, Dakta Mariya Bunkure da sauran manyan ma’aikatan ma’aikatar.
No comments