Daga Aisha Suleman Kaduna A ranar Lahadin da ta gabata ne Makarantar Mu'azu Bin Jabal Lit-tahafizul Qur'an dake Hayin Do...
Daga Aisha Suleman Kaduna
A ranar Lahadin da ta gabata ne Makarantar Mu'azu Bin Jabal Lit-tahafizul Qur'an dake Hayin Dogo Samaru Zaria a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ta yi bikin yaye dalibanta da suka yi haddar Al'kur'ani Mai Girma.
Wakiliyarmu ta sami halartar wajen bikin. Bikin dai an gudanar da shi ne a babban filin dake kusa da harabar makarantar dake Anguwar Makera Kallon Kura Samaru.
Bayan dukkan manyan baki maza da mata iyaye da dalibai har da aminan arziki sun gama samun wajen zama ne sai aka bude taro da addu'a kamar yadda Musulunci ya tanada.
Shi bikin ya kunshi yaye dalibai ne masu sauka da haddace Al'kur'ani mai girma su 57. Masu haddar Alkur'ani mutum 15 duk a wannan makarantar. Abin da ya burge jama'a shi ne samun yaro dan shekara 13 da ya zama gwarzon shekarar 2022 na makarantar.
Yaron Dan shekaru 13 mai suna AbdulHamid Sani Saleh Bichi shi ne yazo na daya a cikin wadanda suka haddace Alkur'ani mai girma, bayan jarabawa da masana kuma gwanaye a bangaren shi haddar Al'kur'ani mai gima a kasa baki daya.
Gwarzon shekarar yayin da yake zantawa da manema labarai ya nuna jindadin matsayi da Allah ya ba shi. Kuma ya yi godiya ga iyayensa da suka bashi kulawa da har ta kai shi ga samun wannan matsayi.
Gwarzon dan shekara 13 ya yi godiya ga malamansu da suka ba shi tarbiya da ya sami haddar Alkur'ani mai girma shima ya yi fatan Allah ya kai kowa gida lafiya.
Shugaban makarantar Ustazz Abubakar Abba a jawabinsa ga dubban mutanen da suka halarci taron, ya fara ne da godiya ga Allah da yin salati ga Annabi da sahabbansa baki daya. Kuma ya yi godiya ga dukkan manyan baki da suka amsa gayyatarsu.
Shugaban ya yabawa dalibai da iyayen dalibai bisa bada goyan baya a dukkan bangarori da suka hadu aka sami nasarar gudanar da wannan biki.
A karshe ya yi kira ga daliban da su zama wakilai masu girmama Alkur'ani a duk inda suke. Kuma ya yi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.
Taron ya sami halartar mai girma Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli da babban Malamin addinin Islama daga jihar Kano Shiekh Daurawa sai babban Darakta a hukumar kula da harkokin addini na jihar Kaduna, Sheikh Abubakar Jamilu Albani Samaru da dai sauran manya daga bangarori da dama a fadin kasarmu Nijeriya. An yi taro lafiya an tashi lafiya.
No comments