Chana ta ce batun 'mamaya' da ake cewa Rasha ta yi a ƙasar Ukraine zancen banza ne kawai kuma salo ne da ƙasashen yamma ...
Chana ta ce batun 'mamaya' da ake cewa Rasha ta yi a ƙasar Ukraine zancen banza ne kawai kuma salo ne da ƙasashen yamma ke amfani da shi wajen sauya zancen gaskiyar abin da yake faruwa.
"Game da ma'anar mamayewa, ina ganin ya kamata mu koma baya domin fahimtar halin da ake ciki a Ukraine a yau. Batun Yukren yana da rikitatten tarihin wanda ya ci gaba har ya zuwa yau. Ba lalai ya zama yadda kowa ke son gani ba ne."
Daga baya ma'aikatar ta ce, babban jami'in diflomasiyya Wang Yi, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin, ya tattauna da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov.
Wang ya ce, batun Ukraine yana da tarihi mai 'sarkakiya', ya kuma nanata cewa, kasar Sin ta fahimci 'damuwar' da Rasha ke da shi kan harkokin tsaro, a cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar.
Sai dai Chana din ta ce akwai buƙatar duka bangarorin biyu da su yi haƙuri; inda kuma ta shawarci 'yan ƙasarta da suke ƙasashen da su zauna a gida; idan har kuma buƙatar fita ya kama dole, to au dauki tutar Chana su rike a hannu su fita da ita.
Chana ta ce tana da bambanci da ƙasashen Yamma masu son zuciya, a don haka ba za su sanya son zuciya ba kamar ƙasashen yamma, za su ci gaba da bibiyar lamuran.
Da take amsa tambayar 'yan jarida ko Rasha ta tuntubi Chana kafin ta kai hari a Ukraine, Chana ta amsa da cewa; Rasha a matsayin na ƙasa mai karfi kuma mai cin gashin kanta ba ta da buƙatar ta tuntu6i Chana akan kudirinta na kare ƙasarta. A don haka a cewarta ba ta bai wa Rasha wani tallatin karfin soji ba.
Mai magana da yawun ma'aikatar lura da ƙasashen waje na ƙasar Chana, Hua Chunying ce ta bayyana haka a yayin taron manema labarai a birnin Beijing a jiya Alhamis 24 ga watan Fabarairun 2022.
No comments