Daga Hussaini Ibrahim Shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Honorabul Shamsuddin Hassan ya tabbatar...
Daga Hussaini Ibrahim
Shugaban kwamitin yada labarai na Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Honorabul Shamsuddin Hassan ya tabbatar da cewa, Mataimakin gwamnan Zamfara, Barista Mahadi Ali Gusau ya cika sharudan tsige shi daga mukaminsa na Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara.
Shamsuddini Hassan ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da ya yi a dakin taron majalisar dokokin jihar Zamfara da ke Gusau.
A Honorabul Shamsuddini Hassan, babu wata kotu da ta aikowa majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin shugaban majalisar, Honorabul Mu'azu Magarya akan kar ta yi aikinta na binciken Mataimakin gwamnan na kin zamansa a Ofishinsa da kuma karkatar da kudin zuwa aljihunsa na ofishin na sa, inji Honorabul Shamsuddin.
Honorabul ya kara da cewa, babu wasu kudi da aka bamu dan mu binciki Mataimakin gwamna, Majalisar na da hurimin tuhumar kiwa a jihar tun daga gwamna har zuwa Masinja muna da ikon kiransa wannan zaure domin ya yi bayani akan abin da ake tuhumarsa akai.
"Don haka mun aikawa Mataimakin gwamna akan ya zo ya kare kansa daga tuhumar da kwamitin kudin na majalisar Dokokin ke masa da kuma kin zuwa aiki amma yaki amsa kiran. Don haka muna tabbatarwa al'ummar jihar Zamfara za mu yi abin da ya dace wanda doka ta aminta da shi wajen ganin mun tsige mataimakin gwamnan nan bada jimawa ba", inji majalisar.
No comments