Daga Hussaini Ibrahim, Gusau A kokarin da gwamna Bello Mohammed Matawale ke yi na ganin ya karawa jami'an tsaro kwarin guiwa...
Daga Hussaini Ibrahim, Gusau
A kokarin da gwamna Bello Mohammed Matawale ke yi na ganin ya karawa jami'an tsaro kwarin guiwa wajen yaki da 'yan bindiga, yanzu haka ya ba iyalan 'yan sanda da 'yan bindiga suka kashe naira Miliyan bakwai inda kowa zai samu naira miliyan daya.
Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba Elkana ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke bada Tallafin kudin da Iyalan 'yan sanda a Hedikwatar 'yan Sanda da ke Gusau.
CP Elkana ya bayyana cewa, wadanda 'yan sandan suka rasa ransu ne a wajen fafatawa da 'yan bindigar wadanda suka hada da manyan Ofisoshin kamar Donal Marcus, Salomon Apere, Steven Higher Nura Ibrahim sai kuma masu mukamin Sajan da suka hada da Abdu Garba, Zubairu Saidu, da Musa Lawal, inji CP Elkana.
Ya kuma kara da cewa wannan tallafin zai karawa Jami'an 'yan sanda kwarin guiwa wajen jajircewa kan yaki da 'yan bindiga da miyagu masu manyan laifuka da ke cikin jihar.
Kuma yanzu haka hukumar 'yan sandan karkashin jagorancin Sufeto Janar Alkali na yake kokarinta na ganin hakkokinsu ya fito dan bai wa Iyalansu .
No comments