DAGA ALI KANO Fim Magazine A daren yau Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta yi taron sulhu tsakanin...
DAGA ALI KANO
Fim Magazine
A daren yau Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta yi taron sulhu tsakanin Ƙungiyar Matan Kannywood (K-WAN) da fitaccen mawaƙin Kannywood kuma jarumi, Naziru M. Ahmad.
Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, shi ne ya kira taron a Kano don sulhunta ɓangarorin biyu a kan rikicin da ya ɓarke a tsakanin su.
Naziru Sarkin Waƙa ya yi iƙirarin cewa a Kannywood ba a sanya mace a fim sai ta bada kan ta.
K-WAN ta ba shi wa'adin kwana uku daga yau ya janye wannan kalamin nasa ko kuma ta maka shi a kotun shari'ar Musulunci a kan tuhumar ɓata suna.
MOPPAN ta yi sauri ta kira taron ne kafin lamarin ya ƙara ƙazancewa.
Shugabar K-WAN, Hauwa A. Bello, da shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Arewa (AFMAN), Sani Sule Katsina, na daga cikin mahalarta taron.
Shi ma Naziru Sarkin Waƙa ya halarta.
Za mu kawo maku cikakken bayanin zaman nan gaba kaÉ—an.
www.fimmagazine.com
No comments