Daga Aisha Suleiman, Zariya Ruth tana daya daga cikin kwararru a kamfanin East West Seed da suka hada guiwa da tsangayar kimiyy...
Daga Aisha Suleiman, Zariya
Ruth tana daya daga cikin kwararru a kamfanin East West Seed da suka hada guiwa da tsangayar kimiyyar aikin gona na Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Wakiliyarmu ta zanta da ita jim kadan bayan kammala taron kuma ta yi karin haske game da taron na su. Ta ce "gaskiya a yau muna farin ciki bisa amsa gayyatarmu da jama'a suka yi kuma muna fatan sakonmu zai je ga sauran al'ummar kasa baki daya", inji ta. Bayan haka ta kara da cewa, "wannan taro ya kunshi yadda ake fitowa da manoma sabuwar fasaha mai sauki ga harkar noma a kasa baki daya. Wannan hanya ta kunshi dubaru iri daban-daban wanda hadin guiwa ne da kamfanoni aikin gona masu gudanar da nazarce-nazarce a kasa da duniya baki daya".
Ta ci gaba da cewa; haka zalika shirin ya kunshi yadda ake bunkasa noman kayan lambu kamar tumatur da kabeji da sauran kayan lambu.
Wannan lokaci a cewarta suna aiki ne da bangarori guda biyar; na farko; Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, sai gwamnatin jihar Kaduna da kamfaninmu na East West Seed da sauransu ke bayar da irin da ake gudanar da shi wannan nazarin. "Kuma a gaskiya wannan gwaji yana fitar da sakamako mai kyau", inji ta.
"Bisa haka ne yasa muka shirya taron baje koli don manoma da masu bincike tare da shaidawa duniya irin ci gaban da aka samu a yanzu. Domin tabbas wannan bincike ya zakulo wa manoma hanyar da za su sami ribar noma a cikin sauki a kuma karamin lokaci", ta tabbatar.
Ruth ta ce yanzu haka sun fito da wani irin tumatur da kwana 60 yake yi a fara dibansa kuma yakan zuba 'ya'ya masu yawa a lokaci kadan.
Ruth ta kara da cewa yanzu haka wanna shiri ya horar da mutane kamar su Dubu Dari (100, 000) a jihohi biyu wato jihar Kano da jihar Kaduna, inda ta ce suna alfahari da hakan a matsayin nasara.
Haka zalika Jami'ar ta yi kira ga manoma da su dawo da hankalinsu ga sabbin dabarun noma su ajiye tsohon tsari, ta ce, yanzu akwai irin Tumatur mai yi akan lokaci kuma akwai irin Albasa mai yi akan lokaci don haka Farfesan ya tabbatar wa manema labarai cewa wannan shiri zai taimakawa Gwamnati wajen kara karfin arziki da samawa mutane aikin yi da za su rika dogaro da kansu ba tare da dogaro da aikin gwamnati ba.
Ruth ta yi godiya ga Sarakuna da manonan da suka sami halartar taron. Jami'ar ta nuna jin dadinta ga dukkan wanda suka sami horon bisa yadda suka bada hadin kai da goyan baya har zuwa wannan rana da aka ba su takardar shaida.
A karshe ta yi fatan Allah ya mayar da kowa gida lafiya.
Hajiya Rabi Yahaya, Malamar gona ce daga jihar Kaduna kuma tana cikin wadanda jihar Kaduna ta turo don su sami karin ilimin aikin gonan don su koyar da wasu a jihar ta su da kasa baki daya. Hajiyar ta nuna gamsuwarsu da horon da suka samu, ta yi godiya ga jihar Kaduna karkashin Gwamna Nasiru Ahmad El-Rufai.
Taron ya sami halartar shugaban Jami'ar Farfesa Kabiru Bala da Farfesa Mahmud Muktar shugaba a wannan yunkuri da Sarakuna da jami'an aikin gona daga cibiyoyi daban-daban a jihar Kaduna da Kano.
An yi taro lafiya an tashi lafiya.
No comments