Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ofishin Jakadancin Nijeriya A Romania Ya Karɓi Ƴan Nijeriya 200 Daga Ukraine

  J akadiyar Nijeriya a Romaniya, Safiya Nuhu.  Jakadiyar Najeriya a Romania da ke makwabtaka da Ukraine ta ce zuwa yanzu sun ka...

 Jakadiyar Nijeriya a Romaniya, Safiya Nuhu. 


Jakadiyar Najeriya a Romania da ke makwabtaka da Ukraine ta ce zuwa yanzu sun karɓi ƴan ƙasar kusan 200 yawancinsu ɗalibai da suka tsallako Bucharest babban birnin ƙasar daga Ukraine.

Safiya Nuhu ta shaida wa BBC cewa suna kyautata zaton samun adadin ƴan Najeriyar fiye da haka da ke tserewa daga Ukraine.

“Mun tarbe su kuma mun ba su masauki a otel otel a Bucharest,” in ji ta.

Ɗaruruwan ƴan Najeriya ne suka tsallaka kan iyakar Ukraine, inda ake sa ran kwashe su zuwa birane mafiya aminci, kafin mayar da su Najeriya.

Sai dai yawancinsu da sauran ƴan Afirka sun yi ƙorafi kan yadda ake nuna masu wariya a kan iyakar Ukraine da Poland.

-Rahoton BBC

No comments