Rfi Hausa ta labarto cewa; kungiyar OXFAM ta gargadi gwamnatin Nijeriya da ta kaucewa shawarar hukumar bada lamuni ta duniya IMF...
Rfi Hausa ta labarto cewa; kungiyar OXFAM ta gargadi gwamnatin Nijeriya da ta kaucewa shawarar hukumar bada lamuni ta duniya IMF wajen gaggauta kara yawan harajin VAT da cire tallafin man fetur da kuma daina banbanta yadda ake sayar da kudaden kasashen ketare.
Kungiyar ta bada shawarar daukar ingantattun matakai na kusa da na nesa wadanda zasu tabbatar da kara yawan kudaden da gwamnati ke kashewa domin bunkasa rayuwar jama’a maimakon dakile kudaden da hukuma ke kashewa.
Daraktan kungiyar a Najeriya Vincent Ahonsi yace kara yawan kudaden harajin VAT da kuma cire tallafin man zai dada jefa ‘Yan Najeriya da dama cikin kangin talauci.
Kungiyar OXFAM ta bayyana cewar mutane biyu da suka fi kowa kudi a Najeriya sun mallaki dukiyar da ta zarce na mutane miliyan 63 dake fafutukar samun abinda za su ci.
Saboda wannan matsayi, kungiyar tace ya dace Najeriya ta mayar da hankali wajen karawa attajiran kasar haraji da kuma karkata kudaden wajen gudanar da ayyukan raya kasa da suka hada da gina hanyoyi, samar da ruwan sha da gina asibitoci da tallafawa manoma da kuma masu bincike akan yadda za’a inganta hanyar noma lura da yadda sauyin yanayi ke illa a duniya.
Shugaban kungiyar yace maimakon dada jefa kashi 99 na ‘Yan Najeriya cikin karin talauci, ya dace hukumomin kasar da su karbi kadan daga cikin arzikin da attajiran kasar suka samu tun bayan barkewar annobar korona.
OXFAM ta kuma bukaci gwamnati da tayi amfani da damar da ta samu wajen yafewa kasar bashin da ake binta ko kuma dakatar da biyan bashin saboda illar da korona tayi wajen ganin an yafe mata baki daya domin yiwa jama’a aiki.
Kungiyar ta kuma bukaci Najeriya ta kara yawan kudaden da take sakawa a hanyoyin kula da ilimi da asibitoci da kuma tabbatar da cewar akasarin kudaden da take kashewa suna isa wajen talaka.
A karshe OXFAM ta bukaci daukar matakan kare lafiya da dukiyoyin jama’ar Najeriya, tare da bunkasa hanyar tabbatar da gaskiya da amana wajen kula da dukiyar jama’a.
No comments