Mai magana da yawun Rasha, Dmitry Peskov. Wasu kadan daga cikin abubuwan da yakamata ku sani dangane da rikicin Ukraine da Rasha...
Mai magana da yawun Rasha, Dmitry Peskov.
Wasu kadan daga cikin abubuwan da yakamata ku sani dangane da rikicin Ukraine da Rasha da ya faru a yau Litinin 28 ga watan Fabarairun 2022.
1. Tarayyar Turai ta kakabawa mai magana da yawun Rasha, Dmitry Peskov takunkumi.
2. An haramta sayar da barasa a Kiev babban birnin Ukraine daga 1 ga watan Maris.
3. Faransa za ta dauke Ofishin Jakadancinta dake Kiev babban birnin Ukraine zuwa garin Lvov dake yammacin Ukraine.
4. Tarayyar Turai na fuskantar ƙarancin makamashi (Energy) sakamakon takunkumin da ta ƙaƙabawa Rasha.
5. Ma'aikatar Harkokin wajen Rasha ta caccaki matakin ƙasar Jamus na tallafawa Ukraine da makamai.
6. Wakilin Rasha a majalisar dinkin duniya ya ce kawancen Ukraine da NATO zai tursasa Rasha ta ƙaddamar da yaƙi.
7. Stan Collymore, tsohon dan wasan Liverpool da Aston Villa ya caccaki 'munafuncin' Tarayyar Turai bisa sanya takunkumi da soke ƙungiyoyin kwallon kafa na Rasha, inda ya ce; "Ba mu kori ma'aikatan Amurkawa daga Birtaniya ba lokacin da Amurka ta mamaye Iraki ba bisa ka'ida ba, don haka me yasa za a hana kowane dan kasar Rasha ikon yin aiki bisa doka," in ji Collymore.
8. Hukumar lura da kafafen watsa labarai na Birtaniya, ta ce za ta ƙaddamar da binciken wadansu shirye-shiryen kafar watsa labaran Rasha mallakin gwamnati.
9. Ƙungiyar kwallon kwando na Tarayyar Turai ta soke huldar dake tsakaninta da Babban Banki na biyu na Rasha, VTB.
10. Zaman sulhun gaba da za a sake tsakanin Rasha da Yukren za a tattauna ne akan muhimman batutuwa da kowa ya kawo a zaman farko da aka yi.
No comments