Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sama Da Mutum Miliyan 14 Ke Fuskantar Barazanar Cutar Dundumi A Zamfara -Kwamishinan Lafiya

    Kwamishinan Lafiya na Jihar Zamfara Aliyu Abubakar na sanya hannun hadin Guiwa da Hukumar Sightsavers domin bada tallafi a j...

    Kwamishinan Lafiya na Jihar Zamfara Aliyu Abubakar na sanya hannun hadin Guiwa da Hukumar Sightsavers domin bada tallafi a jihar. 
 

Daga Hussaini Ibrahim


Kwamishinan lafiya na jihar Zamfara, Alhaji Aliyu Abubakar, a ranar Talata, ya ce, binciken alkalumma da aka gudanar a jihar ya nuna cewa sama da mutane miliyan hudu ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar ta dundumi a dukkanin kananan hukumomi sha hudu na jihar.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a wajen taron tunawa da ranar NTDs ta duniya da ya gudana a dakin taron karo na uku na Hukumar NTDs da aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar Lafiya da ke Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Kwamishinan ya kara da cewa dukkanin jananan hukumomi sha hudu na fuskantar barazanar da cutar yayin da sama da mutane miliyan 4 da ke zaune a jihar ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar ta Dundumi, inji Honorabul Aliyu Abubakar.

Shirin "NTDs na fiye da mutane biliyan 1.7 a duniya ke amfana da shirin. Ya ce yawanci wadanda suka kamu da cutar ta NTD galibi ana nuna musu kyama kuma hakan kadai zai iya yin illa ga wadanda abin ya shafa ko kuma iyalansu.

Ya ce, “Cutar ba ta shafi lafiyar mutane kadai ba, har ma tana dauke musu damar zuwa makaranta ko kuma samun abin dogaro da kai.

"Maganar da ke tattare da hakan na iya yin mummunar tasiri ga wadanda abin ya shafa da kuma iyalansu da al'ummominsu."

Ya kuma yi nuni da cewa gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagoranci Gwamna Matawalle na yin abin da ya kamata wajen ganin an kawar da cutar ta NTD a jihar, inda ya jaddada cewa Nijeriya baki daya musamman jihar Zamfara na cikin hadarin kamuwa da cutar ta NTD.

Ya kara da cewa "kananan hukumomi 7 ke fama da cutar amosanin Ido kuma Dalibai  yara sama da miliyan 1.1 ke fuskantar matsalar ciwon mafitsara.

Shugaban Shirin na Hukumar Sightsavers, Ahmad Ibrahim, ya tabbatar da cewa, Hukumar za ta ci gaba da hada guiwa da ma'aikatar lafiya ta jihar Zamfara, wajen yaki da wadannan cututtuka da suka addabi al'umma.

No comments