Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sanwo-Olu Ya Roƙi Ƴan Majalisar Legas Su Yi Wa Tinubu Aiki Ya Zama Shugaban Ƙasa

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga ƴan majalisar jihar, na jiha da na taraiya, da su yi aiki tuƙuru domin tab...


Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi kira ga ƴan majalisar jihar, na jiha da na taraiya, da su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da burin Bola Tinubu na zama Shugaban Ƙasa.

Sanwo-Olu ya yi kiran ne a yau Juma'a a yayin taron tattaunawa tsakanin ɓangaren zartaswa da na ƴan majalisu a Legas.

Ya ce Tinubu ya sadaukar da kansa ga al'ummar Legas lokacin ya na gwamna da ma ƙasa baki daya, sannan ya samu nasarori da dama.

A cewar Sanwo-Olu, lokaci ya yi da za a rama wa Tinubu irin abubuwan alherin da ya yi wa al'umma, inda ya ƙara da cewa" shi ne mutumin da ya dace kuma ko shakka babu ya fi kowa."

"Ya san matsalolin ƙasar nan kamar yadda ya san bayan hannunsa kuma ya na da sittin da zai magance matsalolin ƙasar.

"Shi ya sanya na ke kiran dukkan mu da mu tabbatar cewa mun yi duk za mu iya a siyasance ko ba a siyasance ba domin mu tabbatar mun taimaka min cicciɓa shugaban ƙasa na gaba wato Bola Ahmed Tinubu," in ji shi.

Sanwo-Olu ya ƙara da kira ga mahalarta taron da su ci gaba da goya wa Jam'iyar APC, inda ya ƙara da kira da a mara wa Tinubu baya domin ya kai Nijeriya zuwa tudun mun-tsira.

No comments