Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Saraki Ya Yi Jawabi A Taron Masu Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Arewa

Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya gabatar da jawabi a taron shekara na masu gidajen talabijin d...


Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya gabatar da jawabi a taron shekara na masu gidajen talabijin da rediyo na arewacin Nijeriya. 

Saraki ya yi jawabi ne yau Litinin, mai taken 'SHAN MIYAGUN KWAYOYI A AREWA, DA RAWAR DA KAFAFEN WATSA LABARAI ZA SU TAKA WURIN DAƘILE ANNOBAR' a wurin taron kungiyar ta NBMOA a ɗakin taro na otal ɗin Bristol dake Birnin Kano. 

Bukola Saraki wanda ya samu wakilcin tsohon kakakin majalisar jihar Kwara, Hon. Ali Ahmed ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai da su tashi tsaye wurin kawo ƙarshen annobar shan miyagun kwayoyi.

Ya ce: "Na yi matuƙar murnar kasancewa a wurin wannan taro na masu juya kafafen watsa labarai a arewacinNijeriya, inda za mu tattauna muhimmin lamarin da ke ci wa kowa tuwo a ƙwarya. 

"Maudu'in wannan taro na yau, yana matuƙar tada min hankali duk lokacin da na tuna da irin illar da yake yi wa al'umma. A matsayina na likita, na san yadda shan miyagun kwayoyi ke tarwatsa al'umma. 

"Ina son tabbatar mana da cewa, shan miyagun kwayoyi na kara ta'azzara annobar garkuwa, ta'addanci da sauran miyagun ayyuka a arewa." Inji shi

Saraki ya kawo alkalumma na yawan waɗanda ke shan miyagun kwayoyi a arewa, inda ya ce a shekarar 2021 an tantance kaso 14.4 na 'yan Nijeriya ke shan miyagun kwayoyi, 'yan shekara 15 zuwa 64. 

Haka nan kuma, tsohon gwamnan na Jihar Kwara ya kawo adadin gidajen gyaran hali da ake da su a faɗin arewa.

Daga ƙarshe ya bayar da misalai na hanyoyin da za a bi wurin saita halin waɗanda suka jefa kansu a wannan mummunar hanya ta shaye-shaye.

 Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya kasance babban baƙo kuma mai masaukin baƙi a wurin taron.

No comments