Shugaban ƙasar Belarus, Alexander Lukashenko ya gargadi ƙasashen yammaci da cewa tarin takunkumi da suke kakabawa ƙasar Rasha na...
Shugaban ƙasar Belarus, Alexander Lukashenko ya gargadi ƙasashen yammaci da cewa tarin takunkumi da suke kakabawa ƙasar Rasha na iya tursasa Rashar ta afka 'yakin duniya na uku.'
“Yanzu ana ta cece-kuce kan harkar banki, Gas, mai, da SWIFT; ya fi yaki muni. Wannan yana jefa Rasha cikin yakin duniya na uku, "in ji Lukashenko a ranar Lahadi, kamar yadda kafafen yada labarai na cikin gida suka nakalto. Ya kara da cewa rikicin nukiliya na iya zama sakamako na karshe.
No comments