Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tashin Farashin Kaya Ne Maƙasudin Ƙara Kuɗin Fiyo-wata -El-Mansur

Daga Idris Umar Kaduna El-Mansur sh ine shugaban kamfani Gidan Ruwa da ake kira El-Mansur Fiyo-wata dake Zariya ta jihar Kaduna....


Daga Idris Umar Kaduna

El-Mansur sh ine shugaban kamfani Gidan Ruwa da ake kira El-Mansur Fiyo-wata dake Zariya ta jihar Kaduna.

Wakilinmu ya nemi jin ra'ayin shugaban da yake masani ne akan Harkar saida ruwan Fiyo-watan. Domin kowa ya saba sayan ruwa akan guda 1 akan Naira 5 musamman a fadin Arewacin Nijeriya kamar jihar Kano da Kaduna amma yanzu ya koma 3 Naira 20 wata Anguwar ma guda 1 Naira 10 ne; to me ya yi zafi ne? Sai El- Mansur ya fara da yi wa manema labarai barka da zuwa.

Bayan haka ya ce dalilin da yasa ruwan ya yi tashin gwauron zabi shi ne, yadda duk magungunan ta ce ruwan ya zama farashinsu ya ninka abin da ake sayensu a baya ya kusan ribi 2 ko 3. Kuma duk wata sana'a ana yin ta ne don riba in babu riba ta koma shiririta ko?

Daraktan ya ce ba a son ransu bane hakan yake faruwa, don haka ya ce jama'a su dai jin haushin kamfanoni ruwa illa dalilin da ya haddasa tashin farashi. Ya ce yanzu kowa yasan yadda farashin wutar lantarki ya koma haka kuma ko ba ka aiki da wuta kana aiki da man fetur ko Dizal duk babu abin da ake samo shi da sauki a cikinsu. Balle shi ruwa na da sinadarai da ba ko'ina ake samunsu ba kamar su (Alif da su kulorin) da dai sauransu.

"A don haka banda ita sana'ar sayar da ruwa tanada matukar muhimmanci a bangaren samun lada shiyasa wasu suka dage kamarmu. Domin ko tsadar leda kawai ta isa fiyo-wata ya kara kudi", ya tabbatar.

Wakilinmu ya tambayi Daraktan to kowacce hanya za a bi talaka ya sami saukin rayuwa ko ta bangaren ruwan sha da ya zama wajibi a yi mu'a'mula da shi? Tambayar da wakilinmu ya kara yi wa Daraktan Gidan ruwa na El-Mansur ke nan.

Sai shi Daraktan ya kada baki ya ce, a gaskiya hanya daya ce wacce za a bi hanyar ita ce gwamnati ta sanya hannu a kowanne bangare na kasuwanci wato a daidaita farashi ga komai. Ya ce, ko kuma Gwamnati ta kawo na ta kayan mai sauki fiye da na ƴan kasuwa.

"Wato idan gwamnati na da kayanta mai kyau tare da farashi ingantacce wanda yake kasa da na ƴan kasuwa to wajibi ƴan kasuwa su tausaya wa kwastoma shi kuma kwastoma sai ya yi adalci", inji shi.

Ƙarshe ne ya yi kira ga ƴa ƴan kungiyar ba su buga ruwan leda wato fiyo-wata da su tausaya kuma su inganta sana'ar ta su don akwai lada a cikinta mai yawan gaske. Kuma ya yi fatan Allah ya sauko da farashi komai a ƙasa baki daya.

No comments