Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsige Mataimakin Gwamnan Zamfara A Yi Hatara Dai -Gwamna Tambuwal

Daga Hussaini Ibrahim Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal kuma mai son tsayawa takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar PDP...


Daga Hussaini Ibrahim

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal kuma mai son tsayawa takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar PDP ya yi kira ga 'yan majalisun Jihar Zamfara da su yi hattara da mutunta shari'a a matsayinsu na masu yin doka wajen tsige Mataimakin gwamnan Zamfara, Barista Mahadi Ali Gusau.

Tanbuwal ya bayyana haka ne a Gusau lokacin ziyarasa ta neman alfarmar 'yan Jam'iyyar PDP da su mara masa baya wajen kudirinsa na fitowa takarar shugaban kasa a zaben mai zuwa.

Gwamna Tambuwal ya kara da cewa, matsalar jihar Zamfara ba ta siyasa bace matsala ce ta magance matsalar tsaro da ta'addan Jihar da yankunan mu dan haka bai kamata ba, wasu su rudi 'yan majalisun wajen ganin sun kawo rudanin siyasa a cikin jihar ba, inji gwamna Tambuwal.

Mataimakin Gwamnan Zamfara yana kotu akan batun da su 'yan majalisar amma suna nema su yi riga Malam Masallaci akan haka ne Tambuwal ya yi kira da su mutunta shari'a karda su bi san rai na wasu a cikin wannan lamarin.

Da ya koma kan takararsa kuwa gwamna Tambuwal ya bayyana cewa, suna neman goyan bayan 'yan Jamiyyar PDP da su sake mara masa baya a karo na biyu dan ya zamo dan takarar shugaban kasa a zaben na shekara ta 2023, dan Jam'iyyar APC ta gaza ta kowanne waje dan haka a shekara ta 2018, muka fice daga cikin ta muka fice daga cikinta muka dawo Jam'iyyar PDP, inji Gwamna Tambuwal.

No comments