Gwamnatin Ukraine ta dage cewar, damar sasanta rikicin da ke ci gaba da ruruwa da Rasha yanzu haka itace hanyar diflomasiyya mai...
Gwamnatin Ukraine ta dage cewar, damar sasanta rikicin da ke ci gaba da ruruwa da Rasha yanzu haka itace hanyar diflomasiyya maimakon tinkarar lamarin da shirin kai harin, yayin da Amurka ta yi gargadin cewa Moscow na kara shirye-shiryen mamaya.
Amurka dai ta ce sakamakon nazarin da ta yi a kan bayanan sirrin da ta tattara na nuni da cewa Rasha na kara azama wajen shirin mamayar Ukraine, kuma yanzu haka ma ta girke kashi 70 na dakarun da take bukata wajen kaddamar da harin.
Jami’an Amurka wadanda suka ce Putin na bukatar dakaru dubu 100 da 50 don aiwatar da mamayar, sun ce hakan na iya kai wa ga karbe babban birnin kasar, Kyiv tare da hambarar da shugaba Volodymyr Zelensky a cikin sa’o’i 48.
No comments