Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Wata Matashiya Ta Rubuta Al'kur'ani Da Hannunta Cikin Wata Uku

Daga Wakilinmu Sumayyah Shuaibu Salisu budurwa ce 'yar kimanin shekaru da ke ajin SS 2 a makarantar Sakandire da ta rubuta A...


Daga Wakilinmu

Sumayyah Shuaibu Salisu budurwa ce 'yar kimanin shekaru da ke ajin SS 2 a makarantar Sakandire da ta rubuta Alkur'ani mai girma da hannunta ba tare taimakon kowa ba a cikin watanni uku.

Yanzu haka dalibar ta kuduri aniyar sake rubuta Qur'anin karo na biyu.

Wannan budurwa 'yar asalin garin Zariya, an haife ta ne a garin Jega, jihar Kebbi, amma ta fara karatu a garin Madina, sa'ilin da mahaifinta, Sheikh Shuaibu Salisu yake can kasar domin koyon karatu a Jami'ar dake Madina.

Da take zantawa da manema labarai a garin Zariya, Sumayyah ta ce "bayan da na haddace Qur'an na kasance mai cike da burin ganin na rubuta Qur'ani da hannu na, don haka na sa lokaci kuma na fara.

"Na kwashe tsawon watanni uku ina rubutawa, kuma hakan na da nasaba ne da rashin lokaci da ni ke da shi. Saboda har yanzu ni daliba ce a ajin biyu na babbar Sakandire (SS2) ga kuma koyarwa ina yi a Al-mu'assasa Al-Islah  Foundation, makarantar da mahaifina ya assasa a Anguwar Dandutse, Sabon Layi Tudun Wada, Zariya.

"Wannan yana cikin dalilan da suka sa na dauki tsawon lokaci ina rubutun, amma ina fata wannan da zan sake rubutawa karo na biyu ba zai kai tsawon lokacin da na dauka a baya ba", inji ta.

Binciken da manema labarai suka yi sun gano cewa Sumayyah ta kasance Alarammiya ga Mahaifinta sa'ilin gudanar tafsir na watan Ramadan ne musamman a lokaci da aka sa dokar hana fita ta lokacin cutar Korona, a 2020, inda take ja masa baki yana fassarawa.

Yanzu haka dai wannan budurwa ta ce tana da sauran buri a rayuwarta; "Ina so in zama kwararriya akan ilmin kwamfuta, sannan in kasance shahararriyar malamar addinin musulunci mai sanar da mutane kalmar Allah." Inji ta.

No comments