Yadda Aka Sallaci Mai Martaba Sarkin Jama'are Alhaji Dr Ahmad Muhammad Wabi III


 Daga El-Mu'az Jama'are

Labarin rasuwar Mai Martaba Sarkin Jama'are dake jihar Bauchi ya riskar da wasu ba'adin al'ummarsa ne tun cikin daren jiya inda wasu kuma sai da safiyar yau Lahadi labarin ya riske su. 

Da misalin karfe 2:00 na ranar yau Lahadi aka sanya domin sallatarsa, domin bada dama ga na nesa su karaso. 


Bayan isowar Gwamnan jihar Bauchi, Sarkin Bauchi, Sarkin Potiskum, Sarkin Katagum, Sarkin Ningi, Sarkin Dass, Sarkin Misau da sauran Sarakuna ne aka fito da gawar Mai Martaba domin sallatarsa. 

Dubban mutane ne maza da mata suka halarci jana'izar. An kuma sallace shi ne a cikin Fadar ta Jama'are tare da dukkan kusoshin gwamnati da manyan Sarakuna. 

Wakilinmu ya labarto cewa tuni dai aka bisne shi a cikin gidansa, inda aka saba binne Sarakunan masarautar. 

Dubban mutane ne suka shiga alhinin rashin, inda mutanen ke ma junansu jaje tare da masa addu'ar neman gafarar Ubangiji. 

Post a Comment

0 Comments