Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Yadda Haɗarin Mota Ya Ci Ran Shugaban Hukumar Zaɓe Ta Zamfara

Kwamishina a Hukumar Zaɓe ta Jihar Zamfara, ZASIEC, Hashimu Gazura ya rasu a wani mummunan haɗarin mota. Gazura ya rasu a shekar...


Kwamishina a Hukumar Zaɓe ta Jihar Zamfara, ZASIEC, Hashimu Gazura ya rasu a wani mummunan haɗarin mota.

Gazura ya rasu a shekaranjiyaJuma'a. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Gazura tsohon ɗan majalisar jiha ne mai wakiltar Mazaɓar Gummi 2.

Mansur Bagudu, Shugaban Hukumar kula da Harkokin Majalisar Dokoki ta Jiha ne ya sanar da rasuwar a wata sanarwa a jiya Asabar.

Ya ce ya rasu ne a wani mummunan haɗarin mota a kan hanyar Yawuri a Jihar Kebbi a ranar Juma'a.

Tun misalin 11 na safiyar yau ne dai a ka yi jana'izar Gazura a fadar Sarkin Gummi.

No comments